Adikon Zamani
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ko kaciyar mata tana da wata illa a likitance?

  • Latsa alamar lasikifa da ke sama don sauraron cikakkiyar tattaunawar da Fatima Zahra Umar game da batun

Na hadu da Hajiya Ladidi, wanda ba shi ne sunanta na gaskiya ba.

Shekararta 39 kuma ga dukkan alamu tana cikin matukar damuwa.

Ta shaida mini cewa an mata kaciya a lokacin tana da shekara 13 da haihuwa, aka kuma yi mata aure tana da shekara 15.

Mutumin da ta aura ya girmeta da shekara 30, a lokacin da aka mata aure, bata iya biya masa bukata ma'ana saduwar aure saboda zafin da take ji a duk lokacin da ya kusance ta.

Sun kasance a haka har shekara guda, wannan dalili ya sa mijin nata ya sake ta.

Wannan dai ya faru ne shekaru da dama da suka gabata.

Yanzu Hajiya Ladidi tana kan aurenta na uku ne, kuma bata canja zani ba, domin har yanzu tana fama da wannan matsalar ta rashin yarda da miji ya kusanceta.

Ta shaida mini cewa har yanzu tana cikin fargabar kaciyar da aka yi mata shi ya sa bata yarda da mijinta.A wannan karon mijinta mai fahimta ne, hakan ya sa yakan fita ya nemi mata a waje don ya biya bukatarsa.Ta ce bata jin dadi kuma tana gani kamar ana cutar ta.

A cikin shirin Adikon Zamani na wannan makon, na tattauna da wata matashiya da itama ka yiu mata kaciyar domin na fahimci yama ake yinta.Itama labarinta kamar na Hajiya Ladidi ne, ma'ana bayan anyi mata kaciyar aka yi mata aure kuma ga mijin da bata so.

Sun fara fuskantar matsala ne tun bayan da ta ki amincewa mijin nata ya kusance ta, hakan ya sa itama ya mayar da ita gidansu.

Na tattauna da wasu wanzamai wadanda suka hakikance cewa, mace ba ta zama cikakkiya idan ba a yi mata kaciya ba.

Abind a suka yi imani da shi shi ne namiji baya jin dadin matarsa matukar ba a yi mata kaciya ba.

Sannan kuma sun ce kaciyar tana ragewa mata sha'awa kuma tana sa su su kame.

A takaice ma dai daya daga cikin wanzaman ya shaida mini cewa matan da ba a yiwa kaciya ba ba za su taba zama masu kame kansu ba.

Likitoci da kungiyoyi masu zaman kansu na daga kan gaba gaba wajen watsi da wannan al'ada ta kaciyar mata saboda matsalolin da ake samu sakamakon kaciyar kamar kamuwa da cutar HIV da ragewa mata ni'ima da dai sauransu.

To amma babban abin shi ne damuwar da matan kan shiga bayan an yu musu kaciyar.

Daya daga cikin batutuwan shi ne matan da ba a yiwa kaciyar ba ba za su taba jin dadin zaman aurensu ba, wanda hakan kuma ba karamin rashin adalci bane.

Don haka a cikin shirin Adikon Zamani na wannan makon mun tambaya shin ko kaciyar mata nada wani alfanu?

Dr Zainab Datti ta asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano ta ce ana yawan samun karuwar matan da ake musu aiki saboda kaciyar da aka yi musu.

Ta kuma tabbatar mini da cewa irin wadannan matan na bukatar shawarwari masu kyau da kuma ta yadda zamu samu nutsuwa a rayuwar aurensu.

A kwanan baya an samu rahoton wata yarinya wadda aka ji mata ciwo sosai saboda kaciyar da aka yi mata.

Mahaifin yarinyar dai ya yi imanin cewa kin yarda da mijinta ya kusanceta da ta yi saboda ba a yi mata kaciyar bane kafin ta yi aure.

Ko da ya ke mahukunta sun shiga maganar inda suka ceto yarinyar har kuma ta warke daga raunin da ta ji.To bayan jin irin wadannan labarai, abin tambayar anan shi ne, shin ko kaciyar mata ta zama dole?

Sai ku sanar da mu abinda kuke ganin.