Hotunan abin da ya faru a Nigeria a makon jiya

Hotunan wasu daga cikin manyan abubuwan da suka faru a sassan Najeriya daban-daban a makon jiya.

Gwamnan jihar Kebbi Abubakar AtikuBagudu tare da Shugaban Kamfanin Mai na Najeriya Mai Kanti Baru, bayan sanya hannu a kan wata yarjejeniyar samar da makamashi daga rake a Abuja ranar Alhamis

Asalin hoton, Kebbi State Goverment

Bayanan hoto,

Gwamnan jihar Kebbi Abubakar Atiku Bagudu tare da Shugaban Kamfanin Mai na Najeriya, Mai Kanti Baru, bayan sanya hannu a kan wata yarjejeniyar samar da makamashi daga rake a Abuja ranar Alhamis

Asalin hoton, Kaduna State Goverment

Bayanan hoto,

Gwamnan jihar Kaduna Nasir el-Rufai yayin da yake sanya hannu a littafin ta'aziyyar tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya Alex Ekwueme a fadar shugaban kasa da ke Abuja. Marigayin ya rasu ne a Landan a farkon makon jiya.

Asalin hoton, Borno State Government

Bayanan hoto,

Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima yayin da yake duba wani aiki a Jami'ar jihar Borno ranar Laraba

Asalin hoton, Nigeria Presidency

Bayanan hoto,

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari lokacin da ya karbi bakuncin Sarkin Benin, Omo N' Oba Uku Akpolokpo Ewuare II, a fadarsa da ke Abuja ranar Alhamis

Asalin hoton, Nigeria Presidency

Bayanan hoto,

Mataimakin Shugaban Najeriya Yemi Osinbajo yayin da ya halarci taron yaye dalibai a cibiyar nazarin manufofi da muhimman bukatu ta kasa (NIPSS) a Kuru kusa da Jos ranar Asabar

Asalin hoton, Nigeria Presidency

Bayanan hoto,

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari lokacin da ya gana da shugabanin Musulmi 'yan darika a fadarsa da ke Abuja ranar Juma'a

Asalin hoton, DG Media

Bayanan hoto,

Gwamnan jihar Gombe Ibrahim Dankwambo da Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sakkawato da kuma Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje a zauren taron ba da kyautukan yabo wanda jaridar New Telegraph ta shirya a jihar Legas ranar Asabar

Asalin hoton, DG Media

Bayanan hoto,

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje tare da mai dakinsa, bayan ya karbi kyautar gwarzon gwamna a bangaren kiwon lafiya da samar da ilimi wanda jaridar New Telegraph ta ba shi a Lagos ranar Asabar