Mata sun fi maza bukatar wa'azi — Sheikh Kabiru Gombe

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Musulunci addini ne na maza da mata – Kabir Gombe
  • Latsa alamar da ke sama don kallon bidiyon hirar

Babban sakataren kungiyar Jama'atu Izalatul Bid'ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS),Sheikh Kabiru Haruna Gombe, ya shaida wa BBC dalilin da ya sa ya ke yawan yin wa'azi a kan mata.

Malamin addinin ya bayyana hakan ne a yayin wata ziyara da ya kai wa BBC a ofishinmu da ke Landan ranar Alhamis.

Ya ce ya fuskanci cewa an bar iyaye mata a baya kuma ba a cika mayar da hankali a kan wa'azin mata ba, a cewarsa.

Ya ce "ko da an yi wa'azi a kan matan, yawanci bai wuce a ce an rataye wata a wuta ba ko kuma malamancin haka, maimakon a tsaya a koyar da su koyarwar addinin Musulunci da kuma yadda za su bauta wa Allah Ubangiji Madaukakin Sarki."

Sheikh Kabiru Gombe ya ce wa'azantar da mace ko ilmantar da ita ya fi muhimmanci a kan na namiji, "domin ita mace makaranta ce guda saboda ita uwa ce kuma ita ce mai tarbiyantar da yara."

Za ku iya kallon cikakkiyar hirar da BBC ta yi da Sheikh Bala Lau da kuma Kabir Gombe idan kuka latsa nan.

Labarai masu alaka