Yadda kek ke hada kan 'yan Nigeria

cake festival
Image caption An bukaci masu yin kate akan su hada kate din da ya nuna muhiman abubuwan da suka faru a Nigeria

An gudanar da taron baje kolin kek domin murnar zagayowar ranar samun 'yancin Najeriya a birnin Abuja.

An nemi masu gasa kek a kan su hada kek din da za su nuna muhiman abubuwan da suka faru a kasar a shekarun baya.

Wadanda suka shirya taron, sun kuma nemi a yi kek da za su yi hasashe game da makomar kasar nan gaba.

Daya daga cikin mutanen da suka shiga gasar, ya hada kek mai bangarori hudu, inda wani bangare an yi masa zanen ganga yayin da dayan ya yi kama da kwallon kafa.

Wadanda suka shirya taron baje kolin sun ce aniyarsu ita ce su nuna al'adun gargajiya na kasar tare kuma da karfafa gwiwar matasa, da kuma hadin kai tsakanin a'lummomi daban-daban ta hanyar hada kek.

Labarai masu alaka