Nigeria: 'Dabi'un iyaye na iya tasiri a gidan auren 'ya'yansu'

Marriage counsel Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Baya ga matsalar mace-macen aure, matsalar fada tsakanin ma'aurata na cikin batutuwa da ke jan hankalin mutane a Najeriya

Dole iyaye su kaurace wa fada ko daukar makami a gaban 'ya'yansu domin gudun kada 'ya'yan su kwaikwayi ko kuma aiwatar da abin da suka gani bayan sun yi aure.

Wannan shawarar ta fito ne daga wani masanin ilimin zamantakewa a Jami'ar Bayero ta kano, Dr Abdullahi MaiKano Madaki.

A hirar da ya yi da BBC, Abdullahi MaiKano Madaki ya ce: 'Shi dan'Adam an halicce shi da dabi'un kallo da sauraro da kuma kwaikwayo. In ya gani zai iya dauka. Idan ya ji, zai iya dauka.'

Ya kara da cewa: 'Iyaye su zauna kan gaskiya bayan an gina aure kan gaskiya, kuma su kasance masu gaya wa kansu gaskiya.

"Abu na biyu da zan dora a kan wannan shi ne idan mutane suka haifi 'ya'ya, to ya kamata a ce duk lokacin da suka samu wani sabani a tsakaninsu, ba a gaban 'ya'yansu za su yi sa-in-sa ko ce-ce-ku-ce ba, balle har a kai ga matakin zage-zage ko doke-doke ko cin mutuncin juna ko ma daukar makami don a illata juna."

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An bukaci ma'aurata da su guje wa aikata abin da za su yi nadama a kai

Malamin ya kara da cewa: 'Idan ku ka bari suna yi za su dauka cewa wannan dabi'a ce mai kyau ko da sun ga kuna yi cikin fushi. Domin akwai matakin da ba za su iya tantance mene ne abu mai kyau kuma mene ne abu mara kyau ba.

"Saboda haka yi a gabansu illa ne. Yi a gabansu na iya sa wa su dauki wani abu wanda ku ba za ku iya sanin sun dauka ba."

Dr Madaki ya ce a gaba idan yaran suka tsinci kansu cikin irin wannan yanayin za su yi kokarin aiwatar da abin da suka gani ba tare da sanin irin illar da za ta haifar musu ba.

Sai dai kuma masanin ilimin zamantakewar ya bukaci ma'aurata su kai zuciya nesa a lokacin da suka yi fushi, kuma su yi tunanin abin da matakin da suke son su dauka ka iya haifar wa domin gujewa nadama.

Latsa alamar lasifikr da ke kasa domin jin yadda hirar da kasance:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
'Dole iyaye su kauce wa fada a idon 'ya'ya'

Labarai masu alaka