Ba za a hukunta Lukaku ba

Romelu Lukaku Manchester United has scored one goal in his last 10 matches for Manchester United
Bayanan hoto,

Romelu Lukaku ya ci kwallo daya a wasanshi goma na karshe da ya buga wa Manchester United

Ba za a dauki kowanne mataki a kan dan kwallon Manchester United Romelu Lukaku ba, a kan zargin da ake na dukan Gaetan Bong a wasansu da Brighton.

Al'amarin ya faru ne a wasan da United ta doke kungiyar da ci 1-0 ranar Asabar, amma kuma alkalin wasa Neil Swarbrick bai gani ba a lokacin.

Hukumar kwallon kafa ta Inglia ta mika lamarin ga wasu tsoffin alkalan wasa uku domin su yi nazari a kai daban-daban.

Dole ne sai kowannensu ya amince cewa laifin da ake zargin ya cancanci kora kafin a dauki mataki a kai, amma kuma hakan ba ta kasance ba.

A yanzu hukuncin da aka yanke na nufin Lukaku ya tsira daga hana shi wasa uku na cikin gida, wanda da an yi masa, ba zai yi wasan United na Premier da Watford da Arsenal da kuma Manchester City ba.

Dan wasan mai shekara 24, wanda yake taka wa Belgium leda ya koma United ne a bazara daga Everton, kuma ya ci kwallo 10 a wasansa tara na farko.

Sai dai kuma a wasansa goma na karshe da ya yi a yanzu sau daya kawai ya ci wa Manchester United kwallo.