'Ana zolayar gwamnatin Buhari kan yaki da cin hanci'

Gwamnatin Muhammadu Buhari ta ce ta kwato makuden kudaden da aka sace Hakkin mallakar hoto MINISTRY OF INFORMATION
Image caption Gwamnatin Muhammadu Buhari ta ce ta kwato makuden kudaden da aka sace

Gwamnatin Najeriya ta koka kan yadda wasu kafofin watsa labarai ke mummunar fassara game da yaki da cin hanci da rashawa da shugaban kasar ke aiwatarwa.

Ministan yada labarai Alhaji Lai Mohammed ya ce kafofin watsa labarai na da 'yancin sukar gwamnati amma bai kamata su rika yi wa gwamnatin shagube ba.

Mr Lai Muhammed ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke jawabi a babban taron kungiyar gidajen rediyo da talbijin na kasar a Abuja.

Ministan ya ce a 'yan kwanakin nan wasu jaridun kasar sun karkata wajen buga kanun labarai dake zolayar yaki da cin hanci da rashawa na gwamnati.

Ya bukaci kafofin watsa labarai da su taimakawa gwamnati wajen yaki da cin hanci da rashawa maimakon su koma gefe a matsayin 'yan kallo.

Alhaji Lai Mohammed ya ce yaki da cin hanci ba zai yiwuwa ba matukar kafofin watsa labarai ba su shigo ciki ba.

Ministan ya ce kuma yi zargin cewa maida hankali ga kura-kuran gwamnati kan yaki da cin hanci da wasu kafofin watsa labarai ke yi tamkar nuna goyon baya ne ga masu satar kudaden gwamnati.

Ya kara da cewa gwamnatin Muhammadu Buhari ta kwato makuden kudaden da aka sace karkashin shirinta na bada tukaici ga duk wanda ya fallasa masu satar kudaden gwamnati.

Labarai masu alaka