Buhari na halartar taron hadin guiwa na AU/EU

Shugaba Muhammadu Buhari zai jaddada kudirin Najeriya na tabbatar da tsaro da zaman lafiya a nahiyar Afrika da tarayyar turai Hakkin mallakar hoto PRESIDENCY
Image caption Shugaba Muhammadu Buhari zai jaddada kudirin Najeriya na tabbatar da tsaro da zaman lafiya a nahiyar Afrika da tarayyar turai

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bar Abuja zuwa birnin Abidjan na kasar Côte d'Ivoire don halartar taron hadin guiwa tsakanin kungiyar tarayyar Afrika da tarayyar turai.

Ana saran shugabannin kasashen Afrika 55 dana tarayyar turai 28 ne za su halarci taron hadin guiwar karo na biyar.

Wata sanarwa daga kakakin shugaban kasar Femi Adesina ta ce ba ya ga shugabannin kasashen, ana saran wakilai daga kasashe mambobin kungiyar da wasu kungiyoyi na kasa da kasa za su halarci taron.

Sanarwar ta kara da cewa shugaba Muhammadu Buhari zai yi amfani da taron na kwanaki biyu don jaddada kudirin Najeriya na tabbatar da tsaro da zaman lafiya a nahiyar Afrika da tarayyar turai.

Hakkin mallakar hoto PRESIDENCY
Image caption Ana saran shugabannin kasashen Afrika 55 dana tarayyar turai 28 ne zasu halarci taron hadin guiwar karo na biyar.

Gwamnonin jihohin Akwa Ibom da Bauchi da wasu ministoci tare da jagoran jam'iyyar APC Bola Ahmed Tinubu ne ke cikin tawagar shugaban kasar.

Labarai masu alaka