Ba zan bi Atiku Abubakar ba — Bindow

Atiku Abubakar Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Atiku ya ce APC ta gaza

Gwamnan jihar Adamawa da ke Najeriya Umar Jibrilla Bindow, ya ce ba zai bi sahun tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar wurin ficewa daga jan'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulkin kasar ba.

A makon jiya ne Alhaji Atiku Abubakar ya fice daga jam'iyyar, yana mai zarginta da rashin cika alkawuran da ta yi wa 'yan kasar da kuma tabbatar da dimokradiyyar cikin gida.

Sai dai gwamnan jihar Adamawa, mahaifar Atiku Abubakar ya shaida wa manema labarai a fadar shugaban kasa cewa ba shi da niyyar yin biyayya ga Atiku Abubakar ta fice daga APC.

Ya bayyana haka ne bayan ganawarsa da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ranar Talata.

Gwamna Bindow ya ce zai ci gaba da kasancewa a jam'iyyar APC har tsawon rayuwarsa.

A cewarsa, "Ina daya daga cikin mutanen da suka kafa jam'iyyar APC. A lokacin da nake dan majalisar dattawa tare da shugaban majalisa na yanzu wanda ya yi bakin kokarinsa wurin ganin dukkan mambobin majalisa da dama sun bi sahu domin kafa APC. Don haka ban ga dalilin da zai sa na fice daga gidan da na gina ba".

"Saboda haka ni dan jam'iyyar APC ne har tsawon rayuwata," in ji shi.

A wata sanarwa da tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar ya fitar tun da fari, ya ce ya bar jam'iyyar APC ne saboda gazawarta wajen cika alkawuran da ta daukarwa 'yan Najeriya na kawo sauyin halin da kasar take ciki.

Ya kara da cewa a shekarar 2013 yana zaman-zamansa jagororin jam'iyyar APC suka same shi da gayyatar ya shiga jam'iyyarsu bayan da aka samu rarrabuwar kai a jam'iyyarsa ta PDP.

Atiku ya kara da cewa an zauna an cimma yarjejeniya kan yadda abubuwa za su kasance don APC ta samu nasara a zaben 2015, amma kuma ba a cika sharuddan ba.

"A kan wannan dalili ne mambobin jam'iyyar APC suka roke ni, da alkawarin kawo gyara a duk wasu abubuwa marasa kyau na rashin adalci, da kuma rashin bin kundin tsarin mulki da PDP ke yi a wancan lokaci."

"A kan wannan dalili ne da kuma alkawura ya sa na shiga jam'iyyar a watan Fabrairun 2014, don a lokacin ba ni da jam'iyya, saboda tabbacin da APC ta ba ni," a cewar sanarwar.

Sanarwar ta ci gaba da cewa: "Duk jam'iyyar da ba za ta kula da al'amuran matasa ba to matacciyar jam'iyya ce. Makomar kasar nan tana hannun matasa ne."

A baya dai Atiku Abubakar ya sha sauye-sauyen jam'iyya daga waccar zuwa wata.

Labarai masu alaka