Gwamnati ta ba 'yar shekara 7 izinin shan wiwi

Ava Barry Hakkin mallakar hoto VERA TWOMEY
Image caption Ava na fama da wata matsananciyar cutar farfadiya ce da ake kira larurar Dravet

Ministan lafiyan Jamhuriyar Ireland ya ba da izini ga wata yarinya 'yar shekara bakwai daga yankin County Cork ta rika samun tabar wiwi don maganin larurar da take fama da ita.

Ava Barry na fama da wata matsananciyar farfadiya da ake kira larurar Dravet.

A ranar Talata ce, Simon Harris ya fada wa majalisar dokokin Ireland wato Dáil cewa ko da yake ba zai iya bayani a kan daidaikun mutane ba, amma ya sa hannu kan bukatar ba da lasisi a karo na uku.

A cikin wani sakon bidiyo mahaifiyarta Vera Twomey na cewa ta ji "labari mai dadi".

"An ba wa Ava lasisin shan wiwi don magani kuma muna nan zuwa gida. Za mu zo gida don bikin kirsimeti, ita kuma tana samun sauki."

Jagoran jam'iyyar Fianna Fáil, Micheál Martin ya fada wa zauren majalisar dokokin cewa a yanzu Ava tana samun kulawa a karkashin wani shiri ta hanyar wani likitan jijiya.

Ya kuma nemi bijiro da wani tallafi don samar da kafa cikin sauri ga kananan yaran da ke fama da farfadiyar da ba ta jin magani.

Ava na fama da farfadiyar da kan shafe tsawon kama daga minti biyu har zuwa sa'o'i kuma zafinta idan ta tashi yakan bambanta.

Gwaje-gwajen da aka yi sun nuna cewa larurar Dravet takan lafa idan an yi amfani da wani nau'in tabar wiwi.

A baya, Misis Twomey ta bukaci majalisar dokokin Jamhuriyar Ireland ta halasta amfani da wiwi a matsayin magani.

A cikin watan Nuwamban 2016, ta fara wani tattaki daga gidanta da ke kauyen Aghabullogue mai tazara zuwa ginin majalisar dokoki a Dublin don bayyana alfanun wannan batu.

Yayin tattakin na tsawon mil 150, ta roki ministan lafiyan Ireland ta ji kukanta a wani sako da ta wallafa ta shafin Facebook.

Ministan Simon Harris ya tuntube ta daga bisani kuma ya sanar da shirin yi wa manufar gwamnati kan amfani da wiwi garambawul.

Labarai masu alaka