An halasta allurar kashe maras lafiya a Australia

Victoria Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Magoya bayan allurar taimaka wa maras lafiya mutuwa sun rungumi juna a zauren majalisar dokokin Victoria makon gobe

Wata jiha a kasar Australia ta halasta taimaka wa marasa lafiya don a kashe shi da allurar mutuwa.

Majalisar dokokin Victoria ta kada kuri'ar amince wa marasa lafiyan da ke fama da cutar ajali, damar su bukaci allurar da za ta karasa su daga watan Yunin 2019.

Yankin Northern Territory mai jama'a nan da can a Australia ne cikin 1995, ya fara ba da hurumi a duniya don marasa lafiya su kashe kansu da taimakon likitoci.

Sai dai majalisar dokokin tarayyar kasar ta kifar da dokar bayan shekara biyu.

Amma a wannan karo, ba ta da ikon sauke dokokin Victoria, jiha ta biyu mafi girma a kasar.

An amince da muhimmiyar dokar ce bayan tafka muhawara tsawon sama da sa'a 100, ciki har da zaman da aka shafe tsawon dare har karo biyu.

Dokar na da nufin ba wa marasa lafiyan da ke fama da cutar da ajali a jiha ta biyu mafi yawan jama'a a Australia, 'yancin gabatar da bukatar a yi musu allurar mutuwa daga tsakiyar 2019.

Ta yi tanadin cewa jazaman ne sai maras lafiya ya kai akalla shekara 18 kuma idan ya rage musu bai fi wata shida da rayuwa a duniya ba.

Firimiyan jihar Victoria Daniel Andrews ya ce "Ina alfahari a yau cewa mun sanya tausayawa cikin tsakiyar harkar dokoki da mulkinmu."

"Siyasa kenan mafi inganci, ita Victoria ke yi wato yin abin da ya dace - jagorantar kasarmu."

Kariya daga azabtarwa

An tsara dokar ce don marasa lafiyan da ke cikin matsanancin ciwo. Tana da matakan kariya guda 68, ciki har da:

Sai maras lafiya ya gabatar da bukata uku ga musammam kwararrun likitoci don su dauki ransa

Sai wani kwamiti na musammam ya yi bitar duk bukatun

Azabtar da maras lafiya yayin daukar ransa zai kasance aikata laifi

Bugu da kari, sai maras lafiya ya zauna a Victoria tsawon akalla wata 12 kuma sai ya kasance yana cikin hankalinsa.

Labarai masu alaka