An 'sassara' wasu yara 'yan Firamare uku a Borno

Maharin ya abka cikin ajin 'yan nazare ne ya kashe yara biyu da kuma wata yarinya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Maharin ya abka cikin ajin 'yan nazare ne ya kashe yara biyu da kuma wata yarinya

Wani mutum dauke da adda ya abka wata makarantar Firamare a jihar Borno inda ya sassara wasu 'yan makaranta uku suka mutu, tare da wata malama.

Lamarin dai ya faru ne da safiyar Alhamis a makarantar Firamaren gwamnati ta Jafi da ke kauyen Kwaya-Kusar a kudancin jihar Borno.

Wani mazaunin yankin da ya je makarantar bayan abkuwar lamarin ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa maharin ya abka cikin ajin 'yan kananan yara ne ya kuma dabawa kananan yara biyu da kuma wata yarinya wuka inda ya kashe su nan take.

Shugaban kungiyar malamai a karamar hukumar Biu, Malam Habu Sulaiman, wanda ya tabbatar wa da BBC abkuwar lamarin ya ce tuni aka mika mutumin ga jami'an tsaro.

Tuni dai aka kai gawar yaran babban asibitin garin Gombe da ke makwabtaka da Kwaya-Kusar.

Wasu rahotanni dai na cewa ana zargin mutumin da ya aikata wannan abu mahaukaci ne.

Rahotannin sun kara da cewa a sakamakon wannan hari dai matasan yankin sun far wa maharin, inda suka yi masa jina-jina har ta kai an mika shi asibiti.

A yanzu dai kwamishinan 'yan sanda na Borno Cp Damian A. Chukwu ya bai wa hukumar 'yan sanda ta Kwaya-Kusar umarni mika maharin ga Hukumar Binciken masu laifuka ta jihar, da su binciki mutumin sosai don a gane halin da lafiyar kwakwalwarsa ke ciki.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A 2014 gwamnatin jihar Borno ta rufe dukkan makarantu a jihar sakamakon hare-haren Boko Haram

A bangare guda kuma wasu mutane da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne sun kai hari inda suka kashe mutum biyu a jihar Adamawa.

An dai kai wannan hari ne da yammacin ranar Laraba a kauyen Wanu kusa da garin Gulak a jihar.

Wannan na faruwa ne kwasa da makwanni bayan wani harin kunar bakin wake da aka kai a wani masallaci a garin Mubi na jihar daya hallaka akalla mutum 50.

Labarai masu alaka