'Likitoci' 400 sun fadi jarrabawa a Nigeria

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Saurari yadda 'likitoci' sama da 400 suka fadi jarrabawa

Sama da mutum 400 daga cikin kimanin 'yan Najeriya 680 da suka karanta aikin likita a jami'o'in kasashen waje ne suka fadi jarrabawar tantance likitoci ta Najeriya.

Sai dai kuma wadanda suka fadi jarrabawar sun ce babu adalci a jarrabarwar suna masu zargin cewa kyashin karantun da suka yi a kasashen wajen ne ya sa aka kayar da su.

Daliban da suka yi karatun likitanci a jami'o'in kasashen wajen dai tare da wasu daga cikin iyayensu sun garzaya zauren majalisar dattawa domin su nemi 'yan majalisar su bi musu kadi kan zargin da suke yi cewa an kayar da su ne a jarrabawar tantance likitoci ta Najeriya.

Daliban sun dauki lokaci suna muhawara a tsakaninsu game da yadda ya kamata su bullo wa matsalar domin samun nasara.

Ko yaya wasu iyayen daliban da suka yi karatun likita a jami'o'in kasashen waje ke ji game da faduwar 'ya'yansu a jarrabawar?

Malam Muhammad Bala Jibrin yana da 'ya'ya biyu a cikin likitocin da suka fadi jarabarar tantancewar.

Image caption 'Likitocin' dai sun garzaya majalisar dattawan Najeriya ne don gabatar da korafin su

Ya ce ''na taba yin aikin kwamishinan ilimi a jihar Bauchi kuma kafin gwamnatin jihar ta kai yara karatu a kasar wajen, sai da suka dauki shugaban hukumar MDCN mai tantance likitoci na wancan lokacin zuwa kasar Misira domin ya amince da yadda ake koyar da aikin likitanci a jami'o'in da za su kai daliban.''

Ya kara da cewa hukumar MDCN ta amince da yadda ake koyar da aikin likitanci a jami'o'in tare da amincewa aikin likitocin kasar Misira.

Daya daga cikin daliban da suka fadi jarabawar, Dr Bashir Isa, ya yi zargin cewa an kayar da su ne ba bisa ka'ida ba.

Image caption Likitocin da suka yi karatu a jami'o'in kasashen wajen sun ce sun sami koyarwar a makarantunsu fiye da irin wanda ake samu a jami'o'in Najeriya

Ya ce: "Ai wannan fadar magana ce kawai. Ta yaya za a ce mutum kusan 700 sun rubuta jarrabawa, kuma wajen mutum 400 da wani abu su suka fadi jarrabawar? Ya kamata a yi tambaya.''

"Na farko dai ka sani wannan jarrabawar tana da sauki ta yadda duk wannan saukin nata kuma aka zo aka ce mun fadi.''

"Sannan inda suke cewa mun fadin shi ya fi ko wane bangare sauki a koyarwar likitanci, shi ne kazo ka yi abu a fili a gani sabanin wani in kace ka tambaye shi ilimi a kwakwalwarsa zai sha wuya kafin ya gaya ma."

Wakilin BBC ya nemi jin ta bakin hukumar MDCN mai tantance likitoci a Najeriya, amma hakar sa ba ta cimma ruwa ba domin jami'ar hulda jama'ar hukumar ta ce ba za ta iya magana kan lamarin ba, kuma bai sami shugaban hukumar, Tajudeen Sanusi, a waya ba.

Rashin tabbatar da kwarewar sama da likitoci 400 dai na zuwa ne a lokacin da Najeriyar ke fama da karancin likitoci.

Labarai masu alaka