Cacar baki ta kaure tsakanin Trump da Theresa May

Trump and May Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Donald Trump da Theresa May a fadar White House a watan Janairu

Shugaba Trump ya ce kamata ya yi fira ministar Burtaniya Theresa May ta mayar da hankali kan abin da ya kira akidojin musulmi na ta'addanci masu mummunar illar da ke faruwa a kasarta maimakon sukarsa.

A sakon tiwitarsa na baya-bayan nan, Mista Trump ya ce bai kamata Theresa May ta yi haushin kaza huce a kan dami ba don kuwa abin da ya yi daidai ne in ji shi.

Shugaban Amurkan ya sake yada hotunan bidiyon tunzura jama'a guda uku da wata kungiyar masu tsananin kishin kasa a Burtaniya ta wallafa.

Sakon tiwitar ya zo ne bayan wani mai magana da yawun fira ministar ya ce ba daidai ba ne Shugaba Trump ya ci gaba da yada bidiyon nuna kiyayya ga musulmi.

Hotunan bidiyon da wata jagorar kungiya mai suna Burtaniya ce Farko na kokarin nuna Musulmai suna ruguza wani mutum-mutumi na kirista da kuma kashe wani yaro gami da far wa wani nakassashe.

Bidiyon wanda Mista Trump mai mabiya sama da miliyan 40 ya sake yada hotunan da Jayda Fransen, mataimakiyar shugabar kungiyar Britain First.

An tuhumi misis Fransen, 'yar shekara 31, a Burtaniya da amfani da "barazana da cin zarafi da zage-zage ko dabi'ar cin zarafi" kan jawaban da ta yi a wani gangami da aka yi a birnin Belfast.

Mijin wata 'yar majalisar dokokin Burtaniya da aka yi wa kisan gilla a baya, Brendan Cox ya fada wa cewa Trump na son "halasta nuna kiyayya" ne

A cewarsa: "Idan wani shugaba ya sake yada bayanan irin wadannan mutane ko ya ba su lasifika ko ya nuna alamun goyon bayansu, abin da hakan ke nufi shi ne halasta ba kawai bayanansu ba har ma da daukacin abubuwan da suka biyo baya."

Amurka da Burtaniya aminan juna ne kuma sau da yawa ana cewa suna da alaka ta musammam da juna. Fira minista Theresa May ce shugabar wata kasa daga ketare da ta fara ziyartar Donald Trump a fadar White House.