Ko me ya sa ake kashe Sufaye a Masar?

Egyptians perform Sufi rituals outside Cairo's Sayeda Zainab mosque, May 2015 Hakkin mallakar hoto KHALED DESOUKI/AFP/Getty Images
Image caption Mabiya darikar Sufi na murnar ranar zagayowar haihuwar Zainab jikar Annabi S.A.W

Kisan mutane fiye da 300 a wani masallaci a tsibirin Sinai na Masar a makon jiya, ya kara jayo hankalin duniya ga halin da Musulmai mabiya darikar Sufi, wadanda aka nufi kai harin a kansu.

Mabiya darikar Sufi sun saba ziyartar iyalan Annabi Muhammad S.A.W da kuma waliyyai, da kuma halartar bukukuwan tunawa da ranar haihuwarsu.

Abin da Sufaye suka fi mayar da hankali a kai shi ne yin Zikiri. Wanda ya hada da ambaton Allah, da karanta ayoyin kur'ani, da kuma yi wa annabi salati.

Kuma suna haduwa su yi Zikiri dhade da wakar yabo da kuma rawa.

Ana samun Sufaye a kasashen Musulmi da ke fadin duniya da suka hada da Sunni da kuma Shi'a.

Sai dai kuma suna samun suka daga mabiya mazhabar Sunni. (Shafi'i, Maliki, Hanafi da kuma Hambali).

A kasar Masar, akwai mabiya Sufi da suka kai kimanin miliyan 15, kuma suna da darika 77.

Babbar darika daga cikinsu ita ce Rifaaiya, wacce take da mabiya kusan miliyan biyu, da kuma al-Azmiya wacce take da mabiya kimanin miliyan daya.

Akwai dubban Masallatai a kasar inda Sufayesuke sallah, kodayake ba duk masallatan ba ne mabiya Sufi.

Sufaye da Masu ikirarin jihadi

Kungiyoyin Salafiyya da na 'yan gwagwarmaya na nuwa adawa ga mabiya Sufi. Inda suka haramta wa mabiyansu yin sallah a Masallatan da suke da alaka da Sufi, kuma suke kallon wakokin yabon da suke yi da wuraren da suke ayyukan ibada a matsayin wani abu da ya saba koyarwar addini.

Kungiyar IS da ke arewacin Sinai ta shafe shekara tana gudanar da gangami a kan mabiya darikar Sufi.

A watan Nuwambar 2016 ne, aka kashe shugabansu mai shekara 98 Sheikh Suleiman Abu Harraz, wanda yake jagorantar mabiya darikar Sufi, bayan da aka sace shi daga gidanshi da ke garin El-Arish.

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Masallacin al-Rawda da ke garin Bir al-Abed inda aka kai hari makon jiya

A Disambar barar ne, jaridar kungiyar IS ta al-Naba ta wallafa wani gargadi ga mabiya darikar Sufi mazauna Masar, da kuma mazauna Sinai a wani bangaren.

Ta ambaci al-Jaririya da kuma wani wurin taronsu wato masallacin al-Rawda a garin Bir al-Abed, inda suka ci alwashin tarwatsa kungiyar.

Sai dai har yanzu kungiyar IS ba ta bayyana cewa ko ita ce ta ke da alhalin kai harin masallacin da aka yi a makon da ya gabata.

Sheikh Khaled shi ne jikan wanda ya kirkiri darikar al-Jaririya, ya ce kashi 90 cikin 100 na wadanda suka mutu mabiyansa ne.

Ya kuma shaida wa BBC cewa a shekarar 1940 aka kirkiri darikar a Sinai, kuma suna Masallatai kimanin 130 a fadin duniya.

Mabiya darikar Sufaye da Siyasa

Shugabannin darikar Sufi sun sha cin gajiyar kawancensu da gwamnatin Masar.

A shekarun 1960 ne, suka hada kai da dan kishin kasa Shugaba Gamal Abdel Nasser, kuma ya yi aiki don ya kara samun daukaka a wurin mabiyansu.

An ci gaba da wannan hadin karkashin mulkin wadanda suka gaji Nasser, Anwar Sadat da Hosni Mubarak.

Bayan juyin juya halin da ya hambarar da Mubarak a shekarar 2011, Sufaye sun shiga siyasa bayan kafa jam'iyyarsu ta Sufi Egyptian Liberation party.

Har ila yau shugabannin darikar Sufi sun goyi bayan sojoji wajen hambarar da gwamnatin Shugaba Mohammed Morsi a shekarar 2013, bayan da aka gudanar da zanga-zangar nuna adawa da mulkinsa, da kuma goyon bayan tsohon soja Abdul Fattah al-Sisi yayin takararsa a shekarar 2014.

Labarai masu alaka