Bosnia: Praljak ya sha guba a gaban kotun duniya

Emergency rescue worker run to the court building in The Hague. Photo: 29 November 2017

Asalin hoton, AFP/Getty Images

Bayanan hoto,

An kira ma'aikatan agajin gaggawa zuwa kotun don su taimaki Slobodan Praljak

Masu gabatar da kara a kasar Netherlands sun tabbatar da cewa wata muguwar guba ce mai laifinnan dan Kuroshiyawan Bosniya, Slobodan Praljak, ya sha a gaban kotu lamarin da ya kashe shi.

Hukumomi a kasar Netherlands sun fara bincike game da yadda wani mai laifi dan Kuroshiyawan Bosniya ya shigar da guba cikin kotun hukunta manyan laifuka ta duniya da ke Hague, kuma ya kashe kansa a zaman daukaka karar da aka nuna kai tsaye a talbijin.

Slobodan Praljak, mai shekara 72, ya mutu a asibiti ranar Laraba jim kadan bayan ya shanye wani abu a cikin kwalba bayan ya yi shelar cewa shi ba shi da laifi.

Wannan ya faru ne jim kadan bayan kotu ta tabbatar da hukuncin daurin shekara 20 da aka yi masa kan laifukan yaki.

Wasu Kuroshiyawa 'yan Bosniya sun yi tsayuwar dare domin tunawa da mutumin da suke yi wa kallon gwarzo.

Firai ministan Kuroshiya, Andrej Plenkovic, ya yi kakkausar suka ga kotun ta musamman ta kasa da kasa mai hukunta manyan laifuka ta tsohuwar kasar Yugoslabiya wadda ta yi masa shari'a.

Shari'ar tabbatar da daurin da aka yi wa Praljak da wasu mutum biyar, ta kawo karshen shari'ar da ake yi a kotun sama da shekara 20.

Ta yaya ya mutu?

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

An ga wata motar daukar mara lafiya a wajen kotun ranar Laraba

Wasu dakiku bayan ya ji cewa karar bai yi nasara a karar da ya daukaka ba, tsohon Janar din ya ce, "Slobodan Praljak ba mai laifin yaki ba ne. Zan yi watsi da hukuncin kotun."

Sannan ya sha guba daga wata kwalba mai ruwan kasa kuma ya yi shelar cewa, "Na sha guba."

Alkalin da yake jagorantar zaman kotun ya dage zaman nata kuma aka garzaya da Praljak asibiti.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Ya yi fama da 'yar gajeriyar rashin lafiya kuma ya mutu a asibitin, in ji mai magana da yawun kotun ICC Nenad Golcevski.

Ya kara da cewa shi ba zai iya tabbatar da abin da ke cikin kwalbar ba.

Mene ne binciken zai mayar da hankali a kai?

A wata takaitacciyar sanarwa, masu gabatar da kara na kasar Netherlands sun ce binciken zai mayar da hankali kan "taimakawa wajen kisan kai da kuma saba wa dokar magani".

Masu bincike za su yi nazari kan wanda ya ba shi magani mai kisa, abin da yake ciki da kuma yadda ya iya shigar da shi dakin shari'ar mai tsananin tsaro, kamar yadda wakiliyar BBC Anna Holligan ta ruwaito daga birnin Hague.

Praljak ba shi ne mutumin da ya fara kashe kansa dangane da wata sharia'a da aka yi a Hague ba.

An taba samun wani dan Kuroshiyawan Sabiya da ake zargi da laifukan yaki Slavko Dokmanovic, ya rataye kansa a shekarar 1998, da kuma Milan Babic wanda shi ma ya kashe kansa a shekarar 2006.