An kama wasu ma'aurata da kyankyasai 200 a akwatinsu

Staff were surprised to find live cockroaches in a couple's hand luggage Hakkin mallakar hoto KANKAN NEWS
Image caption Wata ma'aikaciyar filin jirgin ta ce da ta bude akwatin sai kyankyaso daya ya yi tsalle ya fito ita kuma ta firgita

Jami'an fasa-kwabri a wani filin jirgin saman kasar China sun sha mamaki matuka a yayin da suka bude akwatin wasu ma'aurata suka ga daruruwan kyankyasai masu rai a ciki.

Wata kafar yada labarai ta Beijing Youth Daily, ta ce ma'aikatan tsaro na filin jirgin Guangdong Baiyun sun lura da motsi ne a akwatin dattijan ma'auratan, lokacin da suka ajiye shi a kan na'urar bincike a ranar 25 ga watan Nuwamba.

Watai ma'aikacaiyar tsaro mai suna Xu Yuyu, ta shaida wa kafar yada labarai ta Kankan cewa: "Akwai wani farin akwati dauke da abubuwa masu motsi a ciki."

"Daya daga cikin ma'aikatan ta bude akwatin sai kawai ga kyankyasai suna fitowa. Saura kadan ta yi kuka," in ji Ms Xu.

Da aka tambaye su ko ina za su kai kyankyasan sai mijin ya ce: "Suna amfani da su ne don yin magani, inda za su kwaba da mai a dinga shafawa a jiki."

Beijing Youth Daily ta ce da yake an haramta shiga jirgi da wata halitta mai rai in ba mutum ba, sai ma'auratan suka zabi barin jakar tasu a wajen ma'aikatan.

Sai dai ba a san me ma'aikatan suka yanke shawarar yi da kyankyasai.

Ba wannan ne karo na farko da jam'ian tsaro suka taba kama abun mamaki irin haka ba a wajen bincike.

A watan Agusta ma jami'an tsaro sun gano hannayen mutum a akwatin wani mutum a yayin da ake binciken kayansa.

Hakkin mallakar hoto KANKAN NEWS
Image caption Xu Yuyu ta ce an samu kusan kyankyasai 200 a farin akwatin ma'auratan

Labarai masu alaka