Daliban Nigeria sun koma wanke-wanke a Ingila

Gidauniyar kula da manyan makarantu Tetfund ta tura dalibai fiye da 100 domin yin digirin digir-gir a jam'i'oi a Burtaniya.
Image caption Gidauniyar kula da manyan makarantu Tetfund ta tura dalibai fiye da 100 domin yin digirin digir-gir a jam'i'oi a Burtaniya.

Daruruwan dalibai 'yan Najeriya da ke karatu a jami'o'in kasashen waje karkashin tallafin gwamnati tarayya na fuskantar matsaloli saboda kasa biyan kudin makaranta, inda yanzu wasu daga cikinsu suke kananan sana'o'i kamar wanke-wanke.

Daliban wadanda galibinsu ke shekarar karshe a karatun digirin-digirgir, a yanzu sun soma yin ayyukan hannu don daukar dawainiyar su.

Akasarin daliban sun bar Najeriya ne cike da buri, amma yanzu suna cikin kunci da rashin tabbas inda da dama daga cikin su basa mayar da hankali akan karantun su.

Gidauniyar kula da manyan makarantu wato Tetfund ce ta tura daliban su fiye da 100 domin yin digirin digir-gir a jam'i'oi a Burtaniya.

Kuma gidauniyar ta yi alkawarin biya wa daliban kudin makarantar da kuma na dawainiyarsu.

Sai dai akasarin daliban sun ce gwamnati ba ta cika alkawarin ba.

Tuni wasu jami'o'in suka yi barazanar korar daliban saboda rashin biyan kudin makaranta.

Wata daliba Shakirat Adesola da ke karatu a jami'ar Sussex a Ingila ta shaida wa Aliyu Abdullahi Tanko cewa an ba ta kwanaki don ta biya kudin makaranta ko kuma a kore ta.

Ta ce "a shekarar karatu ta bara ban biya kudin makaranta ba, amma sun ba ni lokaci in biya, kuma a bana sai matsalar ta karu.''

Ta kara da cewa ''daga bisani na bukaci su kara min lokaci, sai dai har yanzu na kasa biyan kudin, a takaice dai an cireni a cikin jerin daliban da suka yi rijista a makaranta."

Image caption Wata daliba Shakirat Adesola da ke karatu a jami'ar Sussex a Ingila

Shi ma wani dalibi mai suna Msugh Targema ya ce ya kusa zautuwa sakamakon wannan matsalar.

Ya ce "sai da na fara sana'ar hannu, na tsawon watanni uku, tun daga karfe uku na asuba nake ta shi barci domin soma aiki.

Ya kara da cewa ''bayan watanni uku ina aiki, sai na ji kamar na fara zarewa, a don haka sai na bar aikin."

Image caption Msugh Targema wani dan Najeriya da ke karatu a jami'ar Sussex a Birtaniya

Mahukunta a jami'ar Sussex dai sun ce suna sane da matsalar da daliban ke ciki kuma suna kokarin taimaka musu.

Sara Dyer mai kula da dalibai 'yan kasashen waje a jami'ar ta shaida wa BBC cewa;

"Jami'ar na taimaka wa daidai gwargwado wajen tuntubar ofishin jakadancin Najeriya a Landon sannan kuma mun bai wa daliban damar su dinga biyan kudin makaranta sannu a hankali.''

Ta kara da cewa ''muna duba yadda za mu iya ba su tallafin kudi iya karfin mu".

Image caption Sara Dyer mai kula da dalibai 'yan kasashen waje a jami'ar Sussex

Daliban dai sun ce sun rubuta wasiku da dama ga hukumomi a Najeriya amma kuma kawo yanzu ba a share musu hawaye ba.

BBC ta nemi jin martani shugabannin a hukumar Tetfund amma abin ya ci tura.

Matukar gwamnatin Najeriya ba ta shigo cikin wannan lamarin ba, makomar karatun daliban za ta kasance cikin wani yanayi na rudani.

Labarai masu alaka