Kofin Duniya: 'Nigeria na da aiki a gabanta'

Kofin Duniya: 'Nigeria na da aiki a gabanta'

Ranar Juma'a ne hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa ta fitar da jadawalin kasashe 32 wadanda za su fafata a Gasar cin Kofin Duniya wanda za a yi badi a kasar Rasha.

Najeriya na cikin rukunin D inda za ta fafata da Argentina, da Croatia, da kuma Iceland.

A cikin watan jiya ne tawagar kwallon kafar Najeriya ta doke ta Argentina 4-2 a wasan sada zumunta da suka buga a kasar Rasha.

Argentina ta samu tikitin zuwa buga gasar kofin duniya da za a yi a Rasha a 2018 daga Kudancin Amurka, yayin da Nigeria za ta wakilci Afirka daga kasashe biyar din da za su je Rasha daga nahiyar.

Masu sharhi kan wasanni suna ci gaba da tofa albarkacin bakinsu kan yadda za a kwashe a rukunin D, musamman ganin yadda Najeriya da Argentina suka saba haduwa a rukuni guda.

Sai dai tarihi ya nuna Argentina ta fi samun galaba a kan Najeriya a karawar da suka yi a baya a gasar.

Karanta wadansu karin labarai