Ana iya zargo surukin Trump kan hulda da Rasha

Michel Flynn
Image caption Michel Flynn ya bayyana cewa yana ba wa masu binciken hadin kai

Tsohon mashawarcin tsaron Amurka, Michel Flynn ya amsa cewa ya zabga wa hukumar FBI karya a bayanan da ya gabatar mata kan tarukan da ya yi da jakadan Rasha kafin Donald Trump ya zama shugaban kasar.

Lauya na Musammam Robert Mueller ne ya gabatar da tuhume-tuhume kansa, a wani bangare na binciken da yake yi kan zargin katsalandan din Rasha a zaben Amurka na 2016.

Mista Flynn shi ne jami'i mafi girma da ya taba rike mukami a gwamnatin Trump wanda kuma aka tuhuma a hukumance ya amince ya ba da hadin kai ga bincike.

Kafofin yada labaran Amurka sun ce Mista Flynn ya shirya ba da shaidar da ka iya zargo Jared Kushner, surukin Trump.

An ba da rahoton cewa guda ne shi cikin manyan jami'an kwamitin karbar mulki da ya umarci Mista Flynn ya tuntubi Rasha.

Michael Flynn shi ne jami'in gwamnatin Trump na farko da aka tuhuma a wannan bincike.

Fadar White House ta ce Flynn bai jingina wa kowa laifi ba sai kansa.

Sanata Mark Warner ya ce yana da ja: "Ba za su iya nesanta kansu daga tsohon mashawarcin tsaron Shugaba Trump ba, wanda ya amsa cewa ya yi laifi. Mu kuma muna d'oki mu ji ko mene ne labarinsa."

Labarai masu alaka