Ba za mu yarda a saba wa Allah a otel dinmu ba – Kungiyar Izala

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
'Mene ne laifi don Izala ta gina otel'
  • Latsa alamar da ke sama don kallon bidiyon hirar

Shugaban Kungiyar Jama'atu Izalatul Bid'ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS), Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya ce bukata ce ta sa kungiyarsu gina otel a Abuja.

Malamin ya bayyana hakan ne lokacin da ya kawo mana ziyara a ofishinmu na Landan a makon jiya tare da rakiyar Sheikh Kabiru Gombe.

Ya ce idan mutane suna ganin kamata ya yi su gina makaranta ko kuma wani abu na daban.

"To a matsayinmu na kungiyar addini muna da wadansu bukatu da suka sha mana gaba wadanda ya kamata a ce mun yi su kafin mu kai wannan," a cewarsa.

Har ila yau, malamin ya ce kafin su gina otel din akwai wata jami'a da kungiyar take kokarin samarwa da kuma kungiyar tana da makarantu da dama wadanda ta gina.

Hakazalika ya ce a matsayinsu na kungiyar addini ba zai yi wu su gina masaukin baki kuma "mu bari a rika saba wa Allah a cikinsa ba."

Za ku iya kallon cikakkiyar hirar da BBC ta yi da Sheikh Bala Lau da kuma Kabir Gombe idan kuka latsa nan.

Ya ce sun gina otel din ne saboda samar wa malamansu masauki yayin da suke Abuja.

"A matsayin malamanmu na addini da sauran al'ummarmu ya kamata a ce muna da kebebben wuri wanda mun tsara shi bisa tsarin addini ba tare da ya saba wa addini ba," in ji shi.

Hakazalika Sheikh Bala Lau ya ce "al'ummar Musulmi suna bukatar wuri mai tsafta irin wannan."

A cikin watan Agustan da ya gabata ne kungiyar ta yi bikin bude otel din wanda aka gina a unguwar Life Camp.

Karanta wadansu karin labarai

Labarai masu alaka