Buhari ya yi Allah-wadai da harin Biu

sojoji na sunturi

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da harin da wadansu 'yan kunar bakin wake biyu suka kai kasuwar Biu ta jihar Borno ranar Asabar.

Bayan ya jajantawa iyalan wadanda abin ya rutsa da su, shugaban ya ce ya yi ammanr cewa dakarun kasar za su samu "galaba kan mayakan Boko Haram wadanda suke kai harin kan mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba."

Wasu mata biyu 'yan kunar bakin wake ne suka kai hari kasuwar Biu a jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya, inda akalla mutum 15 suka rasa rayukansu, ciki har da 'yan kunar bakin waken.

'Yar kunar bakin wanke ta farko ta tayar da bam din da ke jikinta ne a cikin kasuwar Biu "layin 'yan manja da doya," a cewar wani wanda ya shaida al'amarin.

Haka zalika 'yar kunar bakin ta biyu ta ta da bam din da ke jikinta a kusa da kasuwar, wadda take ci a ranar Asabar.

Kakakin rundunar sandan jihar Borno DSP Isuku Victor ya tabbatarwa aukuwar harin, inda ya ce 'yan kunar bakin waken sun kai harin ne da misalin karfe 11:40 na safe a ranar Asabar.

Ya ce bayan mutanen da suka rasa rayukansu, akwai wadansu mutum 53 da suka jikkata.

Karanta wadansu karin labarai

Labarai masu alaka