Za a daure namijin da ya yi saki uku a take a India

A watan Agusta ne aka haramta saki uku nan take
Image caption A watan Agusta ne aka haramta saki uku take yanke a Indiya

Mazan da suka yi wa matansu saki uku a take ka iya fuskantar daurin shekara uku a gidan yari a karkashin wata sabuwar doka da ake nazarinta a Indiya.

Bisa al'ada maza na furta kalmar saki uku lokaci guda ne ta hanyar e-mail ko ta sakon waya ko kuma sauran hanyoyi.

A watan Agusta ne kotun kolin Indiya ta ayyana cewa yin hakan ya saba wa kundin tsarin mulkin kasar, sai dai mahukunta sun ce ana ci gaba da yin hakan.

Har ila yau dokar da aka gabatar ta tanadi tara da kuma samar wa matar da abin ya shafa kulawa.

An aike wa gwamnatocin yankuna daftarin dokar don fara nazari a kanta.

Dokar za ta haramta sakin mata ta hanyar furka kalma saki sau uku lokaci guda.

Kuma ta tanadi cewa idan hakan ya faru ga mace za ta samu kariya ta shari'a.

A karkashin sabuwar dokar ba za a ba da belin mazajen da ake zargi da aikata hakan ba.

Har ila yau dokar za ta haramta yin sakin ta kowacce siga, da suka hada da rubutu a takarda ko kuma ta sakon waya.

Mabiya addini Musulunci na da yawa a Indiya, kuma kasar na daya daga cikin kasashe kalilan da suke saki uku lokaci guda.

Dokar kotun kolin ta biyo bayan karar da wadansu mata biyar suka shigar a gaban wata kotu, inda suke sukar al'adar saki uku nan take wadda a cewarsu ta saba da hakkin dan Adam.

Labarai masu alaka