Man Utd ta lallasa Arsenal

Man U ta lallasa Arsenal da ci 3-1 Hakkin mallakar hoto Julian Finney
Image caption Man U ta lallasa Arsenal da ci 3-1

Mancherster United ta lallasa Arsenal da ci 3-1, a karawarsu ranar Asabar a gasar firimiya.

Alkalin wasa ya ba wa Pogba jan kati a wasan sakamakon ketar da ya yi wa Bellerin a minti na 74 da fara gumurzun.

Har ila yau Newcastle ta sha kashi a hannun Chealsea bayan da aka doke ta da ci 3-1, a wasan da suka fafata ranar Asabar a gasar firimiya.

Dwight Gayle ne ya ci kwallon farko bayan minti 12 da fara wasan, yayin da Eden Hazard ya farke wa kungiyarsa a minti 20 na fafatawar.

Alvaro Morata ne ya zura kwallo ta biyu a ragar Newcastle, bayan da ya doko kwallon da kai a minti na 33.

Daga nan kuma Eden Hazard ya kara kwallo ta uku a minti na 72 da fara gumurzun.

Chealsea tana mataki na uku a teburin gasar da tazarar maki takwas tsakaninta da ta daya wato Manchester City.

Sauran sakamakon wasannin da aka buga a gasar a ranar Asabar

  • Brighton 1- 5 Liverpool
  • Everton 2-0 Huddersfield
  • Leicester 1-0 Burnley
  • Stoke City 2-1 Swansea
  • Watford 1-1 Tottenham
  • West Brom 0- 0 Crstal Palace

Labarai masu alaka