Buhari ya mayar wa Atiku martani

Buhari Hakkin mallakar hoto Getty Images

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce babu wani lokaci da aka taba hana shi izinn shiga wata kasa a duniya, kamar yadda Mai Magana da Yawunsa Femi Adesina ya bayyana a wata sanarwa da ya aike wa BBC.

Shugaban yana mayar da martani ne game da wata hira da jaridar The Boss Newspaper ta yi da tsohon Mataimakin Shugaban Kasar Atiku Abubakar, inda yake cewa an taba hana Shugaba Buhari shiga kasar Amurka.

Dan jarida Dele Momodu ya tambayi Atiku kan jita-jitar da ake cewa an taba hana shi shiga kasar Amurka. Sai dai Alhaji Atiku ya musanta hakan.

Daga nan ne sai tsohon mataimakin shugaban ya ce: "An taba hana Shugaba Buhari shiga kasar Amurka har na kusan tsawon shekara 15 saboda dalilin da suke da alaka da addini."

Har ila yau Atiku Abubakar ya soki gwamnati Buhari kan yadda a cewarsa ta gaza cire wa 'yan Najeriya kitse a wuta.

A watan jiya ne tsohon shugaban ya fice daga jam'iyyar APC. Abin da wadansu suke ganin shirye-shirye yake na kara tsayawa takarar shugabancin kasar a shekarar 2019.

Sai dai bai fito ya bayyana hakan ba tukuna. Hakazalika shi ma Shugaba Buhari bai bayyana anniyarsa ta sake tsayawa takarar ba, kodayake a makon jiya akwai alamomin da suka fara nuna alamar hakan.

Karanta wadansu karin labarai

Labarai masu alaka