Hotunan abin da ya faru a Afirka makon jiya

Wasu zababbun fitattun hotunan Afirka a makon da ya gabata.Wasu zababbun fitattun hotunan Afirka a makon da ya gabata.

Hakkin mallakar hoto Reuters

A ranar Alhamis ne wata mata take rawa a kan titin babban birnin Ivory Coast, Abidjan, yayin da shugabannin Afirka da na Turai suka gabatar da taro, makasudin taron shi ne yadda za a tallafawa matasa sai dai an fi mayar da hankali kan tattaunawa game da yadda ake fuskantar rikicin 'yan ci rani masu tsallakawa wadansu kasashe.

Hakkin mallakar hoto Reuters

A ranar Juma'a ne Habiba 'yar shekara shida ta rungume abin wasanta da aka yi da sukari, wanda ake fi sani da Aroset El Moulid a Tanta da ke arewacin babban birnin Masar wato Cairo. A lokacin da ake bikin murnar zagayowar watan haihuwar Annabi Muhammad S.A.W wanda ake yi duk shekara.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

A ranar Laraba ne Stormzy ya gabatar da shiri kai tsaye a taron da aka yi na zaben fitaccen mawaki namiji, kuma shi ne wanda ya lashe kyautar Mobo ta bana.

Hakkin mallakar hoto AFP

Wadansu matasa yayin da suke wasa a wani sansanin 'yan gudun hijira na Bidi bidi a arewacin kudancin Uganda.

Hakkin mallakar hoto AFP

A ranar Laraba ne wani mutum ya dauki hoto a bikin bude babbar tashar samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana a Afirka ta Yamma.

Hakkin mallakar hoto AFP

A ranar Juma'a ne daya daga cikin mambobin kungiyar mabiya addinin Kirista ta Johane Masowe Vadzidzi VaJesu a Zimbabwe ke jiran rantsar da Shugaba Emmerson Mnangagwa a filin wasa na kasa a Harare.

Hakkin mallakar hoto AFP

An tsaurara tsaro sosai a lokacin bikin rantsar da sabon shugaban kasar Zimbabwe Mista Mnangagwa.

Hakkin mallakar hoto AFP

A ranar Juma'a ne wadansu yara a Morocco suka gabatar da addu'o'in rokon ruwa a babban masallacin Sale da ke kusa da babban birnin kasar Rabat. Sarkin garin ne ya bukaci 'yan kasar su fito su yi addu'o'in don kawo karshen matsalar farin da ake fuskanta a kasar.

Hakkin mallakar hoto AFP

A ranar Laraba ne kungiyoyi wadanda ba na gwamnati ba suka gudanar da aikin ceto a tekun Mediterranean don nemo da kuma lalubo 'yan ci ranin da suka fada.

Hakkin mallakar hoto AFP

Wasu 'yan Afirka da da suke da burin tafiya ci-rani kasashen Turai, maimakon haka kuma ake sayar da su a Libya a matsayin bayi.

Hakkin mallakar hoto AFP

A ranar Talata ne wani ya kai ziyara gidan adana kayan tarihin Masar inda yake kallon gunkin Fir'auna.

Hakkin mallakar hoto EPA

Wani manomi yana tsinkar lemon tanjirin a Boufarik garin da ya shahara wajen noman lemo a kasar Algeria.

Hakkin mallakar hoto AFP

Wadansu yara 'yan Somaliya yayin da suke wasa a gabar tekun Jazera ranar Juma'a.

Labarai masu alaka