Man City ta doke West Ham

City ta buga wasa 13 ba tare da an doketa a bana, Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption City ta buga wasa 13 ba tare da an doke ta a bana

Manchester City ta doke West Ham da ci 2-1 a karawar da suka yi ranar Lahadi a gasar firimiya.

Nasarar da City ta samu ne ya ba ta damar ci gaba da zama ta daya a teburin gasar.

Angelo Ogbonna na West Ham ne ya fara zura kwallo a ragar Manchester City a minti na 44 da fara wasan.

Daga nan kuma Nicolas Otamendi ya farke musu a minti na 57.

Har ila yau kuma David Silva ya kara zabga kwallo a ragar West Ham a minti na 83 inda aka shi wasan 2-1.

City ta buga wasa 13 ba tare da an doke ta a bana, inda take da tazarar maki takwas tsakaninta da mai bi mata baya Manchester United.

Karanta wadansu karin labarai

Labarai masu alaka