"Akwai kalubale a shirin fitar da doya kasashen waje"

Masu fitar da doya kasashen waje sun yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta kawo musu dauki Hakkin mallakar hoto PASCAL DELOCHE /GODONG
Image caption Masu fitar da doya kasashen waje sun yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta kawo musu dauki

Watanni biyar ke nan da gwamnatin Najeriya ta kaddamar da wani shiri na fitar da doyar kasar zuwa kasashen waje, da nufin fadada tattalin arzikin kasar da kuma rage dogaro kan man fetur.

Najeriya dai na noma fiye da kashi 60 cikin 100 na doyar da ake noma wa a duniya.

Shirin fitar da doyar waje ya fi mayar da hankali ne kan kasashen Turai da kuma Amurka.

To shin a ina aka kwana a wannan shiri?

Wakilin BBC Is'haq Khalid ya yi tattaki ya kai ziyara garin Agyaragu da ke jihar Nassarawa, wato daya daga cikin yankunan da ake noman doya domin jin amsar wannan tambaya.

Masu noman doyar sun shaida masa cewa, suna fuskantar kalubale da dama wajen fitar da doyar, don haka suke kira ga gwamnatin tarayyar da ta shigo ciki domin agaza musu.

Mr Vincent Yandev Fama-Abi, na daga cikin mutanen da ke fitar da doyar zuwa kasar waje ya kuma shaida wa wakilin namu cewa, "kawo yanzu na samu damar fitar da tan 76 na doya zuwa kasar Amurka.

"Amma babban kalubalen da irinmu-irinmu masu fitar da doya ke fuskanta shi ne na kudi, don haka da gwamnati za ta karfafa wa bankuna su taimaka mana da lamuni za mu ji dadi, kuma zai yi kyau idan gwamnati ta hada hannu da kamfanonin fito domin su rage mana farashin fitar da kayan"

Gwamnatin Najeriya dai na fatan kasar za ta iya samun kudi kimanin dala biliyan shida a duk shekara daga fitar da doya zuwa kasashen waje, da kuma samar da ayyukan yi ga dubban mutane.

To sai dai kuma wani hanzari ba gudu ba shi ne, kimanin kashi 30 cikin 100 na doyar da ake nomawa a kasar na rubewa, saboda kasar ba ta da nagartattun wuraren ajiya, sannan kuma tsarin sufurin kasar ma ba shi da kyau.

Masu sukar lamirin shirin fitar da doyar zuwa kasashen waje dai sun ce, kamata ya yi gwamnati ta kafa kamfanonin sarrafa doya a cikin kasar ta yadda za a rika fitar da abubuwan da ake sarrafawan zuwa kasashen waje, a maimakon a rinka fitar da ita kanta doyar.

Labarai masu alaka