Jarumin fina-finan India Shashi Kapoor, ya mutu

Sashi Kapoor Hakkin mallakar hoto BBC Hindi
Image caption Yana cikin fitattun jaruman fina-finai na Indiya da suka yi fice a baya

Fitaccen Jarumi da kuma mai shirya fina-finan Indiyan nan, Shashi Kapoor, ya mutu yana da shekara 79.

Kapoor, wanda ya fito a fina-finai masu farin jini kamar Deewar da Kabhie Kabhie, ya shafe wani lokaci yana jinya a asibiti.

Sashi Kapoor daya ne daga cikin iyalan Kapoor da suka mamayi fagen fina-finan Indiya na gomman shekaru.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shashi Kapoor ya mutu yana da shekara 79 a duniya

Ya ci kyaututtukan fina-finai da yawa a kasar Indiya ciki har da kyautar Padma Bhushan da gwamantin Indiya ta ba shi a shekarar 2011.

Ya kuma fito a wasu fina-finan Amurka da na Birtaniya.

Mista Kapoor ya fara aikinsa na fim ne tun yana yaro kuma ya fito a fina-finai sama da 150, ciki har da fina-finan Ingilishi 12.

An san Kapoor da murmushi mai jan hankali kuma sau da yawa masu sha'awar fina-finansa sukan siffanta shi a matsayin tauraron da ya fi kowa kyau.

Ya fito a fina-finai tare da taurari irin su Amitabh Bachchan a cikin manyan fina-finan na shekarun 1970 da kuma shekarun 1980, kuma jaruman biyu suna fitowa a matsayin 'yan-uwa da kuma abokai na kut-da-kut.

Kalamansa na "Mere paas maa hai" (Ai ina da goyon bayan mama) - a fim din Deewar a lokacin wani tayar-da-jijiyar-wuya da dan'uwansa na fim Amitab Bachchan, na daya daga cikin maganganun da aka fi so daga fina-finan Bollywood a fadin duniya.

Hakkin mallakar hoto INDRANIL MUKHERJEE
Image caption Shashi kapoor ya yi fice a fina-finan Bollywood