'An kashe' tsohon shugaban Yemen, Ali Abdallah Saleh

File photo showing Yemen's ex-president Ali Abdullah Saleh (R) delivers a speech in Sanaa, Yemen (24 August 2017) Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Ali Abdullah Saleh became an ally of the Houthis after Yemen's civil war began in 2015

Rahotanni daga Yemen na cewa an kashe tsohon shugaban kasar Ali Abdullah Saleh, a wani fada da aka tafka da tsoffin abokansa.

Kafafen yada labarai da kungiyar 'yan tawaye ta Houthi ke iko da su sun ambato jami'ai na ayyana "kawo karshen cin amanar kasa da mayakan sa kai ke yi da kuma kashe shugabansu."

Wasu majiyoyi daga jam'iyyar General People's Congress ta Mista Saleh sun tabbatar da mutuwarsa, a cewar gidan talbijin na Al Arabiya.

Hotuna da bidiyon da ake ta yadawa a intanet sun nuna gawar wani mutum da ke kama da Mista Saleh da wani mummunan rauni a kansa.

Har a makon da ya gabata, magoya bayan Mista Saleh sun yi ta fafatawa da mayakan Houthi a wani yaki na adawa da shugaban kasar Yemen mai ci yanzu Abdrabbuh Mansour Hadi.

Amma tashe-tahsen hankulan da ake kara samu da kuma sabani kan yin iko da babban masallacin da ke yankin da 'yan tawaye ke iko da shi a Sanaa, babban birnin kasar, ya jawo mummunan fadan da ya yi sanadin mutuwar mutum 125, inda mutum 238 kuma suka ji rauni tun ranar Larabar da ta gabata.

A ranar Asabar ne, Mista Saleh ya nemi ya sauya yanayin da ake ciki tsakaninsa da gamayyar kawancen da Saudiyya ke jagoranta, idan har ta daina kai hari Yemen.

Gamayyar kawancen da kuma gwamnatin Mista Hadi sun yi maraba da kalaman. Amma mayakan Houthi sun zarhi Mista Saleh da son yin juyin mulki a kan kawancen da bai taba yin amana da shi ba.

Fiye da mutum 8,670 ne suka mutu, wasu 49,960 kuma suka jikkata, tun bayan da gamayyar kawancen ta shiga cikin yakin basasar da aka fara a watan Maris din 2015, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

Rikicin da kuma kawanyar da aka yi wa kasar sun tagayyara mutum miliyan 20.7 masu tsananin bukatar agajin gaggawa, al'amarin da ya jawo suka shiga halin tsananin rashin abinci da duniya ba ta taba fuskantar irinsa ba, ya kuma jawo barkewar amai da gudawa da ya yi sanadin mutuwar mutum 2,211 tun watan Afrilu.

Labarai masu alaka

Karin bayani