Buhari na ziyara a Kano a karon farko tun da ya hau mulki

Buhari a Kano
Image caption Kano dai ita ce cibiyar siyasar shugaban

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya isa jihar Kano da ke arewacin kasar, a karon farko tun bayan da ya zama shugaban kasa sama da shekara biyu da suka wuce.

Kano dai ita ce cibiyar siyasar shugaban.

Shugaban dai ya samu tarbar gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje da ministan harkokin cikin gida, Abdul-Rahman Dambazau, da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II da sauran manyan mutane a filin jiragen sama na Aminu Kano da safiyar Laraba.

Wata sanarwa da mai bai wa shugaban kasar shawara kan shafukan sada zumunta Bashir Ahmad ya wallafa a shafinsa na Twitter ta ce, Shugaba Buhari "zai yi ziyarar kwana biyu a jihar Kano, babbar cibiyar siyasarsa da inda babu wanda ya isa karawa da shi".

Bayanan da BBC ta samu sun nuna cewa Shugaba Buhari zai gana da manyan mutane da dama da kuma kaddamar da ayyukan da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya aiwatar.

Image caption Shugaba Buhari yana ziyarar aiki ta kwana biyu a Kano

Sai dai mazauna jihar da dama na sukar shugaban saboda abin da suka kira rashin kulawa da jihar da kuma gudanar da ayyukan gwamnatin tarayya duk da ikirarin da yake yi na kaunarta.

Amma wasu magoya bayansa na ganin ko da bai kai ziyara jihar ba, babu abin da zai shafi irin kaunar da suke yi masa.

Yadda Kanawa suka zabi Buhari

Irin kuri'un da suka kada masa a 2015

9,401,288

Yawan al'ummar Kano

  • 2,172,447 Yawan kuri'un da aka kada a zaben 2015

  • 1,903,999 Kuri'un da Buhari ya samu

  • 215,779 Kuri'un da Jonathan ya samu

Ofishin Shugaban Najeriya

Tun gabanin zuwan shugaban dai aka tsaurara tsaro a jihar, kana aka rika sanarwa a gidajen rediyo cewa iyaye su ja kunnen 'ya'yansu da su guji tayar da hatsaniya a lokacin ziyarar shugaban kasar.

An kuma bai wa makarantun cikin birni da kewaye umarnin rufewa na kwana biyu, wato Laraba da Alhamis, don a rage cunkoson ababen hawa yayin ziyarar shugaban.

Wasu masu sharhi a kan sha'anin siyasa na cewa masoyan Shugaba Buhari da gwamnatin Kano za su yi matukar farin cikin ziyarar tasa za ta sa masu yi musu shagube su rufe bakunansu.

Ku latsa alamar lasifikar da ke kasa don sauraron rahoton da abokin aikinmu Ibrahim Isah ya hada mana kan wannan ziyara:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Rahoton Ibrahim Isa kan ziyarar Buhari a Kano

Labarai masu alaka