Ma'aikatan jami'a na yajin aiki a Najeriya

Galibin daliban jami`ar Bayero ta Kano suna hutu Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Galibin daliban jami`ar Bayero ta Kano suna hutu

A Najeriya kungiyar ma`aikatan jami`a ta umurci `ya`yanta da su fara wani yajin aikin na kasa baki daya.

Kungiyar dai ta ce ba ta da zabin da ya wuce yajin aiki, sakamakon zargin da ta ke yi cewa gwamnatin ta gaza wajen cika wasu alkawuran da suka cimma a baya.

Daga cikin alkawuran har da batun biyan wasu kudadensu na alawus.

Wakilin BBC daya ziyarci jami`ar Bayero ta Kano ya ce yajin aikin na shafar daliban da ke gab da kammala karatunsu.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kungiyar dai na zargin gwamnati da rashin maida hankali wajen inganta fanni ilimi a Jami'a

A baya dai mambobin kungiyar sun zargi gwamnati da rashin maida hankali wajen inganta fanni ilimi a Jami'a.

Sai dai Ministan ilimi Malam Adamu Adamu ya kare gwamnati daga zargin yi wa ilimin jami'a rikon sakainar kashi.

Yajin aikin ma'aikata ya zama tamkar ruwan dare gama duniya a Najeriya.

A lokuta da dama ma'aikata a jami'a kasar na shiga yajin aiki ne domin neman abin da suke kira hakkokinsu.

Labarai masu alaka