Annobar sankarau ta hallaka mutum 20 a Nijar

Jami'an kiwon lafiya na ci gaba da samar da allurar rigakafi ga wadanda suka kamu da cutar. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Jami'an kiwon lafiya na ci gaba da samar da allurar rigakafi ga wadanda suka kamu da cutar.

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar sun ce akalla mutum 20 ne suka mutu sakamakon kamuwa da cutar sankarau a kasar.

Cutar dai ta bulla ne a wani kauye mai suna unguwar Mallam da ke yankin Mirriah a jahar Damagaram.

Wakiliyar BBC Tchima Illa Issoufou wacce ta ziyarci garin ta ce ta tarar iyalai na zaman makokin wadanda suka mutu a gidaje da dama.

Wasu mazauna garin sun ce akasarin wadanda suka mutu sakamakon kamuwa da cutar mata ne da kananan yara.

A halin yanzu jami'an kiwon lafiya na ci gaba da samar da allurar rigakafi a cibiyoyi da aka kafa don kula da wadanda suka kamu da cutar.

Labarai masu alaka