Nigeria: 'Yan kasuwar da suka yi asara za su dara

Shaguna da dama sun kone kurmus sakamakon gobarar da ta tashi a kasuwa Sabon Gari da ke birnin Kano
Image caption Za a bayar da tallafin kudi ga 'yan kasuwar da suka yi asara sakamakon gobara a jihar Kano

A yau ne gwamnatin jihar Kano da ke arewacin Najeriya, za ta fara ba da tallafi ga `yan kasuwar da suka yi fama da iftila`in gobara tun daga shekara ta 2015.

Za a dai bai wa kowanne dan kasuwa kashi biyar cikin dari ne na gwargwadon abin da ya yi asara.

'Yan kasuwar za su samu wannan tallafin ne bayan shafe lokaci mai tsawo suna jiran tsammani.

To sai dai kuma, gwamnatin jihar ta ce an samu jinkirin bayar da tallafin ne sakamakon jinkirin da wasu masu bayar da gudunmuwa suka yi wajen cika na su alkawarin.

Kazalika tsarin da aka bi ma wajen tantance ainihin wadanda suka yi asarar, shi ma na daga cikin abin da ya haifar da jinkirin saboda a cewar gwamnatin jihar ta Kanon, abu ne da ke bukatar taka-tsan-tsan.

Gwamnatin ta ce yanzu komai ya kammala inda za a fara ba wa 'yan kasuwar da suka yi asarar tallafin.

Kwamishinan yada labarai na jihar, Malam Muhammad Garba, ya shaida wa BBC cewa," Gwamnati za ta rarraba wannan tallafi da ya kai na naira biliyan daya da miliyan dari uku da talatin da uku da aka tara lokacin da aka kaddamar da asusun neman tallafin a karkashin shugabancin Alhaji Aliko Dangote".

A nasu bangaren gamayyar kungiyoyin 'yan kasuwar jihar Kano ta bakin shugabansu Alhaji Uba Zubairu, ya ce " Sun yi wa Allah godiya, tun ana cewa ba za a yi ba, to yau gashi an yi, kuma bisa la'akari da yadda gwamnatin ta yi tsarinta, ba na jin za a cuci wani wajen bayar da tallafin domin cekin kudi ne za a ba ka sai kaje banki ka karbi kudinka lakadan".

Alhaji Uba Zubairu, ya ce bisa yanayin da ake ciki a kasa baki daya na matsin tattalin arziki, to ayi hakuri da kashi biyar din da za a ba wa wadanda suka yi asarar domin da ba bu gara ba da di.

Fiye da 'yan kasuwa dubu biyar ne za a ba wa tallafin wadanda suka yi asara sakamakon masifar gobara a kasuwar Sabon Gari da Singa da 'yan katako da Kurmi da kuma kasuwar Farm Centre, duka a birnin Kano.

Labarai masu alaka