Rochas na shan suka kan nada kanwarsa kwamishiniyar walwalar ma'aurata

Okorocha Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A watan Octoba ma Mista Okorocha ya yi ta shan suka sakamakon gina mutum-mutumin shugaba kasar Afirka ta Kudu, Jacob Zuma na tagulla

Ce-ce-ku-ce ya barke a shafukan sada zumunta da muhawarar Najeriya, kan nadin da gwamnan jihar Imo da ke kudancin kasar ya yi wa kanwarsa, na kwamishiniyar jin dadi da walwalar ma'aurata.

A ranar Litinin ne Gwamna Rochas Okorocha ya nada sabbin kwamishinoni 28, da shugabannin kwamitin mika mulki 27 da kuma shugabannin kananan hukumomi 27 a jihar.

Mutane na ta tafka muhawara ne kan nadin da Mista Okorocha ya yi wa kanwar tasa, inda da dama ke ganin babu wani abun burgewa wajen kirkiro sabon matsayin na kwamishiniyar jin dadi da walwalar ma'aurata, yayin da wasu kuma ke cewa bai kamata ya bai wa kanwar tasa Mrs. Ogechi Ololo nee Okorocha, mukamin kwamishiniya ba.

Misis Ololo dai mata ce ga wani injiniya Chuks, wanda dan majalisar wakilan tarayya ne, kuma ta rike mukamai da dama tun bayan zamowar dan uwanta gwamna a shekarar 2011, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Kafin a nada ta kwamishiniyar jin dadi da walwalar ma'aurata dai, tana rike da mukamin mataimakiyar shugaban ma'aikatan gidan gwamnati da kuma mai ba da shawara ta musamman kan al'amuran cikin gida ga gwamnan.

Buhari zai ziyarci yankin jihohin Igbo - Rochas Okorocha

Mutum-mutumin Zuma: Okorocha na shan suka

Wannan batu na nadin da Mista Okorocha ya yi wa kanwar tasa a matsayin kwamishiniyar jin dadi da walwalar ma'aurata, kusan shi ne ya mamaye kafofin sada zumunta a Najeriya a ranar Talata, musamman ma shafin Twitter.

Hakkin mallakar hoto Twitter
Image caption Ire-iren sakonnin da mutane suka yi ta wallafawa a shafin Twitter dangane da batun

Wasu ma'abota amfani da shafin sun wallafa sakonni kamar haka @UrbanCulture06: "Gwamna Rochas Okorocha na jihar Imo ya nada kanwarsa Ogechi a matsayin kwamishiniyar jin dadi da walwalar ma'aurata..... Mutanen Imo ya ya jikinku?"

@Les_munches ya rubuta cewa:"Ina so na zama kwamishinan kula da gumaka. Don Allah ku yi ta yada sakon nan ko zan yi sa'a ya kai ga Rochas Okorocha har ya bani aiki."

"Okorocha ya nada kanwarsa Ogechi Ololo (nee Okorocha) a matsayin kwamishiniyar jin dadi da walwalar ma'aurata? Manta da batun son-kan da ya nuna don wannan ya zama ruwan dare a gwamnatin tarayya da ma jihohinmu, amma mene ne amfanin kwamishiniyar jin dadi da walwalar ma'aurata? Al'ummar Imo gaskiya gwamnanku ba shi da lafiya sam-sam." @ogundamisi

Hakkin mallakar hoto Twitter

Sai dai wasu sun kwatanta nadin da Mista Rochas ya yi wa kanwar tasa da cewa ko a kasashe irin su Hadaddiyar Daular Larabawa UAE ma, an nada ministar jin dadi da walwala.

Amma da dama sun soki hakan da cewa UAE kasa ce da ta riga ta ci gaba kuma al'ummarta ba sa cikin kunci kamar a Najeriya.

Wannan ne dai karo na farko da aka taba bayar da irin wannan mukami na ma'aikatar jin dadi da walwalar ma'aurata, wanda jihar Imon ta yi.

A watan Octoba ma Mista Okorocha ya yi ta shan suka sakamakon gina mutum-mutumin shugaba kasar Afirka ta Kudu, Jacob Zuma na tagulla tare da sanya wa wani titi sunansa, a matsayin karrama shi.

Hakkin mallakar hoto Twitter

Labarai masu alaka