'Atiku Abubakar zai kawo rigima a PDP'

PDP ta ce ba za ta ba Atiku takara ba tare da ya cika sharudanta ba Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption PDP ta ce ba za ta ba Atiku takara ba tare da ya cika sharudanta ba

Wasu manyan 'yan jam'iyyar PDP a jihar Adamawa da ke Najeriya sun ce tsohon mataimakin shugaban kasar Alhaji Atiku Abubakar ya koma jam'iyyar ne domin ya haddasa husuma a cikinta.

Dr Umar Ardo, daya daga cikin delegate-delegate din da za su wakilci karamar hukumar tsohon mataimakin shugaban kasar, Jada, a babban taron jam'iyyar da za a gudanar a karshen makon nan ne ya bayyana haka a hirarsa da BBC.

Tsohon mataimakin shugaban kasar dan asalin karamar hukumar ta Jada ne.

Dr Ardo ya ce "Atiku Abubakar bai dawo PDP bisa gaskiya ba, bai dawo bisa tsarin mulki ba, bai dawo bisa kan doka ba. Kuma ya dawo ne saboda bisa bukatun kansa... domin ya kawo rigima".

A cewarsa duk da yake Atiku Abubakar da magoya bayansa za su karawa jam'iyyar PDP karfi "amma kuma akasari za su kawo jam'iyya ne rashin zaman lafiya saboda jama'arsa za su so taimaka masa wajen biyan bukatun kansa.".

Babban jam'in na PDP ya kara da cewa tsohon mataimakin shugaban kasar ba zai iya kwace ikon jam'iyyar daga hannunsu ba, yana mai cewa amma "zai kawo tangarda da fadace-fadace da kuma tashin hankali" lamarin da zai yi tarnaki ga ci gaban jam'iyyar.

A ranar Lahadi ne Atiku Abubakar ya bayyana komawarsa jam'iyyar PDP a shafinsa na Facebook.

Ya zargi jam'iyyar APC da kin cika alkawuran da ta yi wa 'yan kasar, yana mai cewa: "Gwamnatin APC ta yi alkawarin samar wa mutum miliyan uku aiki a ko wacce shekara amma mutum miliyan ukun ne suka rasa aikinsu a lokacinta".

Sai dai bai fito fili ya bayyana anniyarsa ta sake neman shugabancin kasar a babban zaben kasar na shekarar 2019 ba.

Ya ce ya koma jam'iyyar ne saboda matsalolin da suka sa ya fice daga PDP a shekarar 2014 "an warware su yanzu."

Sai dai har zuwa lokacin wallafa wannan labari gwamnatin Shugaba Buharin ba ta mayar da martani ba.

A nata bangaren, jam'iyyar PDP ta bakin shugabanta na riko, Sanata Ahmed Makarfi ta ce tana murna da komawar Alhaji Atiku cikinta ko da yake ta kara da cewa babu tabbacin cewa za ta ba shi tikitin yin takara a karkashinta a zaben 2019 sai ya cika sharudanta.

Labarai masu alaka