'Daura dankwali na maganin cutar Asthma'

Wata mata ta rufe baki da hanci da gyale lokacin sanyi. Hakkin mallakar hoto ASTHMA UK
Image caption Lullube baki da hanci na taimakwa wajen dumama iska mai sanyi da masu Asthma ke shaka

Ana fadakar da masu fama da ciwon shessheka, ko Asma, amfanin rufe hanci da baki da gyale domin kaucewa tashin ciwon lokacin sanyi.

Wata kungiyar agaji a Biritaniya ta ce bincike ya nuna cewa, shakar sanyi ko iska mai tattare da ruwa na toshe mashigar iska a makogoro, wanda hakan ke ta'azara mutum uku cikin hudu da ke dauke da cutar ta Asma.

Lamarin na sanya mutane tari da atishawa da kuma shidewa.

Kungiyar agajin na amfani da maudu'i mai taken #Scarfie, wajen fadakarwa a shafukan sada zumunta, amma kuma suna karawa da cewa yafa gyale na iya ceto rayuwa amma ba zai maye gurbin maganin asma ba.

Mutum miliyan hudu da ke dauke da cutar asma a Biritaniya sun ce shakar iska mai sanyi lokacin hunturu na ta'azzara masu ciwon.

Ethan Jennings, daga Lancashire, wanda ya kusa shekara hudu, na fama da asma tun yana jariri.

A shekara daya kawai an garzaya da shi asibiti cikin gaggawa sau 17.

Mahaifinsa Trevor, ya ce lokacin hunturu ba ya masa da dadi.

Hakkin mallakar hoto ASTHMA UK
Image caption Ethan na da wata 11 lokacin da numfashinsa ya soma shidewa

Ya ce, "lokacin sanyi, ya fi fuskantar matsala, kuma alamun ciwon sun fi fitowa."

A yanayin hunturu da ya cika shekara daya ne ya fi muni, - "saura kiris mu rasa shi," in ji Trevor.

Ethan ya shafe mako guda a asibiti rai hannun Allah, ana faman nema masa lafiya.

Tun daga nan dai ya samu lafiya, amma kuma iyayensa na sa masa ido kwarai lokacin hunturu.

Mahaifinsa ya ce, "Ina sauraron na ji wani dan tari. Saboda maganarsa bai kai ya iya gaya mana idan yana jin zafi a kirjinsa ba, amma muna sa ido."

Ya kara da cewa, "yanzu dai muna iya kokarinmu musamman idan ya fita waje."

Iska mai dumi

Dokta Andy Whittamore, babban likitan ciwon Asma a Biritaniya, ya ce fita waje ma kadai lokacin sanyi zai iya zama barazana ga rayuwar mai cutar asma.

Ya ce, "Zama a Biritaniya na nufin babu halin kaucewa sanyi lokacin hunturu, amma idan duk mutumin da ke da asma, ya dan lullube hancinsa da bakinsa da gyale, hakan zai dumama iskar kadan kafin ya shake ta, wanda hakan zai rage barazanar tashin asmar."

Likitan ya kara da cewa, "Muna bayar da shawara ga al'umma- da masu cutar asma da ma wadanda basu da ita - a yada sakon nan na cewa mafi saukin abu kamar gyale na iya ceton rayuwa".

A Biritaniya, mutum kusan miliyan 5.4 na fama da ciwon asma, miliyan daya daga cikinsu kuma yara ne.

A makon da ya gabata kuma mutum 1,410 ne suka mutu sakamakon cutar, -14 daga cikinsu kuma yara ne.

Labarai masu alaka