An saki fursunoni 500 a Kano yayin ziyarar Buhari

Shugaba Buhari ya nuna takaicin yadda akasarin fursunonin matasa ne Hakkin mallakar hoto NIGERIA PRESIDENCY
Image caption Shugaba Buhari ya nuna takaicin yadda akasarin fursunonin matasa ne

Gwamnatin jihar Kano ta saki fursunoni 500 yayin ziyarar da shugaba Muhammadu Buhari ke yi a Kano.

Shugaban kasar wanda ya shaida sakin fursunonin a babban gidan yari na Kurmawa da ke Kano ya bayyana takaicinsa kan yadda ya ga akasarin fursunoni matasa ne.

Shugaba Buhari tare da gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje sun jaddada aniyar gwamnati wajen rage cunkuso a gidajen yarin kasar.

An dai zakulo fursunonin 500 da suka hada da maza da mata ne daga gidajen yari daban-daban na jihar Kano.

A halin yanzu ana tsare da fursunoni 1,398 ne a gidan yari na Kurmawa mai cin mutum 750.

Wannan ne karon farko da Shugaba Muhammadu Buhari ke ziyara a jihar tun bayan da ya dare kan karagar mulki a 2015.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nemi sauran gwamnoni su yi koyi da gwamnan jihar Kano wajen gudanar da ayyukan ci gaban jihohinsu.

A wani takaitaccen jawabi da ya yi a wurin kaddamar da asibiti a ungunwar Giginyu da ke tsakiyar birnin, Shugaba Buhari ya ce irin wadannan ayyuka suna kawo sauyi sosai a rayuwar al'umma.

A nasa jawabin, Gwamna Ganduje ya yaba wa shugaban kasar bisa ziyarar da yake yi a jihar.

Labarai masu alaka