Trump ya debo ruwan dafa kansa — Hamas

Shugaban Trump ya ce Amurka za ta goyi bayan masalaha ta hanyar samar da kasashe biyu matukar Israila da Palasdinawa sun amince. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shugaban Trump ya ce Amurka za ta goyi bayan masalaha ta hanyar samar da kasashe biyu matukar Israila da Palasdinawa sun amince

Kungiyar Hamas ta ce shugaba Donald Trump ya kwanto kura bayan sanarwa da ya yi cewa Amurka ta mayar da birnin Kudus a matsayin babban birnin kasar Isra'ila.

Shi dai Mr Trump a lokacin da yake jawabi a fadar White House, ya bayyana matakin a matsayin wani abu da aka dade ba a yi ba a kokarin karfafa zaman lafiya a yankin Gabas Ta Tsakiya.

Shugaban Trump ya ce Amurka za ta goyi bayan masalaha ta hanyar samar da kasashe biyu matukar Israila da Palasdinawa sun amince.

Jim kadan bayan sanarwa Firai Ministan Israila Benjamin Netanyahu ya fito ta gidan talbijin inda ya bayyana matakin a matsayin wani babban abun tarihi.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Benyamin Netanyahu ya yai marhabin da matsayin shugaban Amurka, Donald Trump

Mr Netanyahu ya kuma jaddada cewa Israila ba za ta sauya yanayin da ake ciki ba a birnin Kudus wanda ya kunshi wuraren ibada na Yahudawa da Kirista da kuma Musulmai.

Ya ce ''muna matukar godiya ga Shugaban saboda jarumtakarsa da kuma adalar shawarar da ya yanke ta amincewa da Kudus a matsayin babban birnin Isra'ila.''

Ya kuma kara cewa shawarar bude ofishin jakadancin Amurka a can alama ce ta kudurin shugaban na yin riko da dadaddiyar gaskiya amma mai dorewa, da cika alkwuran da ya yi, da kuma bunkasa zaman lafiya.

Sai dai kakakin kungiyar Hamas na Palasdinawa ya ce matakin tamkar tsokanar fada ce kawai wanda babu abun da zai haifar illa fitina a yankin.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kungiyar Hamas ta Palasdinawa ta dade tana gwagwarmaya da makamai

Shi ma shugaban kungiyar kwato 'yancin Falasdinawa Saeb Erekat ya ce Shugaba Trump ya wargaza masalahar da ake nema ta hanyar samar da kasashe biyu.

Ya ce daga yanzu Amurka ba ta cancanci wani matsayi ba a yunkurin da ake yi na samun zaman lafiya a yankin.

A nasa martanin, babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, ya bayyana halin da ake ciki a matsayin zaman zullumi, inda ya ce babu wani zabi da ya wuce a samar da kasashe biyu.

Labarai masu alaka