Kasashen duniya sun yi caa kan Trump

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Shugabannin duniya sun yi wa Trump kashedi kan Kudus

Kasar musulmi mafi girma a duniya, Indonesiya da kuma Malaysiya sun bi sahun kasashen manyan aminan Amurka wajen la'antar matakin Shugaba Trump na amincewa da Kudus a matsayin babban birnin Isra'ila.

Kawayen Amurka tun tale-tale ciki har da Burtaniya da Faransa da kuma Saudiyya sun yi tir da matakin.

Saudiyya ta bayyana matakin Trump a matsayin rashin sanin ciwon kai kuma wani gagarumin koma baya ga shirin samar da zaman lafiya.

Iran ta yi gargadi game da barkewar wata sabuwar zanga-zangar kwatar 'yanci ta Intifada.

Bangarorin al'ummar Falasdinawa sun yi kira a gudanar da yaje-yajen aiki da jerin zanga-zanga.

Wata wakiliyar BBC ta ce matakin abin fargaba ne ga Falasdinawa, don kuwa suna son Gabashin Kudus da ke karkashin mamaya, bayan Isra'ila ta kwace shi a yakin Gabas ta Tsakiya cikin 1967 ya zama babban birnin kasarsu ta gaba.

Ya zuwa yanzu Isra'ila ce kadai ta yi maraba da shawarar Trump.

Firai minista Benjamin Netanyahu ya ce shawarar Shugaba Trump ta bayyana Kudus a matsayin babban birnin Isra'ila wani "abin tarihi" ne.

Image caption Taswirar birnin Kudus

Kungiyar hada kan kasashen Larabawa za ta yi wani taron gaggawa a ranar Asabar mai zuwa.

Yayin ake sa ran Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai yi nasa taron ranar Juma'a bayan kasashe wakilansa takwas sun bukaci haka.

Shugaba Trump ya sauya manufar wajen Amurka tsawon shekara da shekaru inda ya amince birnin Kudus da ake takaddama kan shi a matsayin babban birnin Isra'ila.

Ya ce shawarar ta yi la'akari da zahirin kasancewar Isra'ila a birnin, amma dai ya ce shata takamaiman kan iyakoki, wani batu ne na Yahudawa da Falasdinawa.

Ya kuma ce za a mayar da ofishin jakadancin Amurka zuwa Kudus daga birnin Tel Aviv, don cika alkawarinsa na yakin neman zabe.

Duniya ba ta taba daukar Kudus a matsayin yankin Isra'ila ba, yayin da Falasdinawa ke kallon Gabashin birnin a matsayin babban birnin kasarsu da za a kafa.

Hakkin mallakar hoto AFP/GETTY IMAGES
Image caption Falasdinawa masu zanga-zanga sun kona hotunan Donald Trump a Gabar Yamma da Jordan

Labarai masu alaka