Ko malalar fetur na kashe yara a Nigeria?

Ko malalar fetur na kashe yara a Nigeria?

Nigeria na fuskantar daruruwan malalar mai a duk shekara, akasarinsu kuma na faruwa ne a yankunan da mutane ke noma ko kuma suke rayuwa.

Wani sabon bincike da masana kimiyya suka yi a jami'ar St Gallen da ke Switzerland ya ce malalar mai ka iya yin sanadiyyar mutuwar kananan yara.

BBC ta je yankin Niger Delta don ganawa da wasu iyalai dake zaune a wani gari da malalar mai ya mamaye.