Kotu ta ki bayar da belin wadda ake zargi da kashe mijinta

Maryam rike da jaririyarta a kotu
Image caption Maryam rike da jaririyarta a kotu

A ranar Alhamis ne aka ci gaba da zaman shari'ar da ake yi na matar da ake zargi da kashe mijinta, Maryam Sanda, a wata babbar kotun birnin tarayyar Najeriya, Abuja.

A watan Nuwamba ne dai aka gurfanar da Maryam a gaban kotun bisa zarginta da kashe mai gidanta, Bilyaminu Bello, bayan ta daba masa kwalba a kirji.

A zaman shari'ar na ranar Alhamis, Maryam ta tsaya a gaban mai shari'ar rike da carbi a hannunta.

Sai dai alkalin ya dakatar da ci gaba da shari'ar saboda a cewarsa, sai 'yan sanda sun kawo wasu mutum uku da ake zargi da jirkita hujjojin da za su iya taimakawa wajen gano yadda aka kashe Bilyaminu.

Wadannan mutum ukun sun hada da wata Maimuna Aliyu da Safiya Aliyu, wadanda ake kyautata zaton makusantan Maryam ne.

Sai dai 'yan sandan sun ce ba su samu damar aikewa da mutanen sammaci ba ne, shi ya sa ba su gurfana a gaban kotun ba.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Kotu ta ba da umarnin tsare Maryam a gidan yarin Suleja

Amma alkalin ya ce bai ga wata alama da ke nuna cewa 'yan sandan sun yi iya kokarinsu da ke nuna cewar sun aike wa da mutanen sammaci ba.

Masu shigar da karar dai sun yi alkawarin cewa za su kawo mutane ukun da ake zargi da jirkita hujjojin ranar 14 ga watan Disamba, inda za a ci gaba da sauraron karar.

A wannan karon dai wani sanannen lauya mai suna JB Dawudo ne yake kare Maryam a shari'ar, kuma ya nemi alkali ya bayar da belinta zuwa ranar da za a sake zaman kotun.

Sai dai alkalin kotun Yusuf Halilu, ya yi watsi da bukatar lauyan, inda ya ki bayar da belinta, amma ya ba shi damar ganawa da ita na tsawon minti 20 kafin a wuce da ita gidan yarin Suleja.

Abokin aikinmu Abdulwasi'u Hassan, wanda ya halarci zaman kotun, ya ce Maryam ta shiga kotun dauke da jaririyarta 'yar wata takwas wadda take ta tsala kuka.

Kazalika ya ga Maryam ta shiga motar gidan yarin da jaririyar tata karkashin rakiyar ma'aikatan gidan yari.

Labarai masu alaka