Israel: An yi arangama a Yammacin Kogin Jordan kan birnin Kudus

Bayanan bidiyo,

Rikici ya barke a Bethlehem

A kalla Falasdinawa 16 ne suka ji rauni a wani tashin hankali da aka yi a Yammacin Kogin Jordan, yayin da ake zanga-zangar nuna adawa da matakin da Shugaban Amurka Donald Trump ya dauka na mayar da Kudus babban birnin Isra'ila.

Rahotanni sun nuna cewa mutane sun samu raunukan ne sakamkon jefa musu hayaki mai sa hawaye da harsashin roba, amma an ji wa mutum daya rauni sakamakon harbinsa da aka yi da harsashi.

Isra'ila ta girke karin daruruwan dakaru a Yammacin Kogin Jordan.

Sanarwar da Mista Trump ya yi dai ba ta samu karbuwa ba a duniya baki daya, inda ake yin tur da hakan saboda sauya tsarin Amurka na gomman shekaru a kan wannan lamari mai sarkakiya.

Falasdinawa mazauna Yammacin Kogin Jordan da Zirin Gaza sun mamaye tituna don gudanar da zanga-zanga.

Mafi yawan abokan Amurka na kut-da-kut sun ce ba su yarda da matakin ba, kuma Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar kasashen Larabawa za su yi taro nan da kwanaki masu zuwa, don mayar da martani kan batu.

Akwai fargaba cewa sanarwar za ta iya sabunta barkewar fada. Kungiyar Falasadinawa ta Hamas tuni ta yi kira da a yi zanga-zangar Intifada.

Me Trump ke cewa?

A ranar Laraba ne shugaban Amurka ya ce ya yi amanna lokaci ne ya yi na mayar da Kudus babban birnin Isra'ila.

"Na dauki wannan mataki ne don kare martabar Amurka da kuma neman kawo zaman lafiya tsakanin Yahudawa da Falasdinawa," in ji shi.

Ya ce ya umarci ma'aikatar harkokin wajen Amurka da ta fara shirin mayar da ofishin jakadancinta Kudus daga Tel Aviv.

Duk da gargadin rashin zaman lafiya da za a iya samu a yankin, matakin ya zama cikar alkawarin da Mista Trump ya dauka ne a lokacin neman zabensa.

Ya kara da cewa: "Mayar da Kudus babban birnin Isra'ila ba wani ba ne face amincewa da abun da ya kamata a yi a zahiri.

"Kuma abu ne da ya kamata a yi."

Mista Trump ya ce Amurka za ta goyi bayan samarwa kasashe biyu mafita.

Abin da ke nufin samar da hanyar sasanta rikicin kasar Falasdinu cikin kan iyakar da aka sani kafin a tsagaita wuta a shekarar 1967 a gabar Yamma da Kogin Jodan da Zirin Gaza da kuma gabashin birnin Kudus, wadda za ta zauna cikin lumana da kasar Isra'ila - idan duka bangarorin biyu suka amince da hakan.

Shugaban ya kuma ki yin amfani da da kalaman da Isra'ila take amfani da su wajen siffanta birnin Kudus a matsayin babban birnin kasarta har abadan wadda ba za a raba ba.

Falasdinawa suna son gabashin birnin Kudus ya zama babban birnin kasar Falasdinu ta gaba.

Martani

Firayim ministan Isra'ila, Benyamin Natanyahu, ya ce Isra'ila ta matukar gode wa Mista Trump, wanda ya hada kansa har abadan ga tarihin babban birnin kasar.

Ya kara da cewa Isra'ila "tana magana da sauran kasashen domin su bi sahun Amurka. Ba na shakkar cewa sauran kasashe za su mayar da ofisoshin jakadancinsu birnin Kudus - lokacin yin hakan ya zo."

Bai ambaci ko daya daga cikin wadannan kasashen ba, duk da cewa an ambaci kasar Philippines da Jamhuriyar Czeck a kafafen watsa labaran Isra'ila.

Bayanan hoto,

Manyan wuraren Ibadah a birnin Kudus

Mutane a bangaren Falasdinawa ba su da irin wannan tunanin.

Ismail Haniyeh, shugaban Hamas wadda take gudanar da lamura a Zirin Gaza, ya yi kira da a yi zanga-zangar Intifada a ranar Juma'a, kuma ya ce ya kamata "ranar ta zama ranar farko ta bore ga 'yan kama wuri zauna."

"Mun bai wa dukkan 'yan Hamas umarnin cewa su shirya domin bin dukkan umarnin da za a ba su domin tinkarar wannan muhimmiyar barazanar," ya fadi hakan ne a wani jawabin da ya gabatar a Gaza.

Jam'iyyar Alfatah ta Shugaban Falasdinawa, Mahmoud Abbas, tana neman ta nuna rashin jin dadinta ta hanyar diflomasiyya, ta hanyar shigar da kara a Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya tare da neman kungiyar kasashen Larabawa ta tsaya tsayin daka.

"Za mu ayyana Amurka a matsayin wata kasa da ba ta cancanci wadda za ta dauki nauyin duk wani shirin samar da zaman lafiya ba," in ji mai magana da yawunsa Dr. Nasser Al-Kidwa.

"A zukatanmu ta rasa iya aiwatar da ko wane abu kan wannan lamarin."

Wadanne kasashe ne suka yi tir da matakin Trump?

Bayanan bidiyo,

Shugabannin duniya sun yi wa Trump kashedi kan Kudus

An yi ta Allah-wadan matakin a kasashen Larabawa da kuma kasashen Musulmi, inda Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ke gargadin cewa (Trump) yana son "ya yi wa yankin kawanya da wuta."

Shugabannin Birtaniya da Faransa da Turai dukkansu sun ce sun ki amincewa da sanarwar Amurka.

Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, ya ce matakin ya ci karo da dokar kasa da kasa da kuma yarjejeniyoyin Majalisar Dinkin Duniya.

Me ya sa sanarwar ta ke da muhimmanci?

Birnin Kudus yana da muhimmanci ga 'yan Isra'ila da Falasdinawa. Birnin na kunshe da wurare masu tsarki na manyan addinai guda uku - Yahudanci da Islama da addinin Kirista.

Ikon Isra'ila kan birnin Kudus ba abu ne da kasashen duniya suka taba yarda da shi ba, kuma dukkan kasashe suna da ofisoshin jakadancinsu a birnin Tel Aviv.

Wadanne hanyoyi ne mafita bayan mafitar samar da kasashe biyu?

Abin da ya sa kama wuri zaune ke da wuya.

Isra'ila ta kwace gabashin birnin Kudus, wanda ya hada da tsohon birni, bayan yakin kwana shida na shekarar 1967, amma kafin yanzu kasashen duniya ba su amince cewa yana jikin Isra'ila ba.

Yarjejeniyoyin zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Falasdinawa sun nuna cewa za a tattauna makomar birnin Kudus a karshe-karshen tattaunawar zaman lafiya.