Wata ta cizge wa saurayinta maraina

CIARAN DONNELLY Hakkin mallakar hoto CIARAN DONNELLY
Image caption Kotu ta ce dole Nunzia Del Viscio ta rika zama a gida babu yawo nan da can tsawon sa'a takwas har wata shida

An umarci wata mata ta biya tsohon saurayinta diyya bayan ta sa hakora ta gartsa masa cizo kuma har ta farka masa fatar maraina, ya fito.

A cikin watan Mayun 2016 ne, Nunzia Del Viscio, 'yar shekara 43, ta kai wa saurayin wannan farmaki a gidansa da ke Edinburgh cikin Burtaniya.

Ita dai ta ce ta yi hakan ne don kare kanta, duk da haka an same ta da laifin far wa mutum..

An sanya Nunzia Del Viscio tarnakin walwala tsawon wata shida, inda ala dole ake bukatar ta kasance a gida daga tsakanin karfe 10 na dare zuwa karfe 6 na safe.

Da ta bayyana gaban kotun Edinburgh ranar yanke hukunci, an umarci Nunzia ta biya tsohon saurayin diyyar fam 500.

Alkali Peter McCormack ya saurari cewa mutanen da abin ya shafa 'yan kasar Italiya ne, kuma dukkansu na aiki ne a gidan abinci da ke Edinburgh.

'Farfasa kayan daki'

Del Viscio, da Mista Palma da kuma sauran mutum biyu sun gamu a wani gidan rawa bayan sun tashi daga aiki. Inda suka sha barasa kuma har ita Nunzia Del Viscio ta ce ta hada da shan kwaya.

Bayan an tashi daga gidan rawa, sai mutanen hudu suka tafi gidan Mista Palma a cikin taksi.

Palma ya fada wa kotu cewa da wayewar garin ranar, sai Nunzia Del Viscio ta fara "farfasa" kayan daya daga cikin dakunan gidan.

Ya ce ya shaida mata cewa ta yi hakuri ta tafi, amma kawai suna musayar yawu sai ta kafa baki ta gartsa masa cizo a daya daga cikin marainansa, har sai da ya fito waje.

"Na yi kokari na dakatar da jinin da yake zuba da tawul, kuma na kira motar daukar marasa lafiya," in ji shi.

Daga nan sai aka dauke shi zuwa asibiti, inda aka mayar masa da dan marainin kuma aka yi masa dinke-dinke.

'Yan sanda sun ga Nunzia Del Viscio a wajen gidan Mista Palma ga jini kace-kace a hakora da bakinta.

'Matukar gigicewa'

Nunzia ta ji raunuka a idonta kuma ta kukkurje a fuskarta, inda ta cewa 'yan sanda Palma ne ya doke ta.

'Yan sanda suka ce ya yi matukar gigicewa, kuma sun samu dakin kwanansa a hargitse, ga kuma jini ya malala a kasa.

Yayin shari'ar, lauya mai kare wadda ake zargi Philip Templeton, ya tambayi Palma ko shi ne ya raunata Nunzia a ido da fuska.

Ya amsa cewa shi ne, amma ya yi ne lokacin da yake kokarin hana Nunzia Del Viscio dukansa.

Ta fada wa kotu cewa ta so fita daga gidan ne, amma sai Palma ya hankado ta ta fadi a kasa kan sumunti daga nan kuma ya bi ta ya rika naushi.

Nunzia Del Viscio ta ce: "Da ya taso min ne sai na cije shi. Ina iya tuna jinin da na ji kawai na shiga hanci da bakina."