An kama yaron da ya yankewa mahaifiyarsa kai a China

Map showing Wenxing in Sichuan in China

An kama wani yaro mai shekara a China kan zarginsa da kashe mahaifiyarsa da kuma yanke mata kai.

Rahotanni sun ce yaron ya nadi bidiyon kisan da ya yi mata tare da sanya wa a shafin sada zumunta na WeChat.

Kwanaki kadan bayan hakan ne aka kama shi bayan da wani abokinsa ya nuna wa mahaifiyarsa bidiyon.

Lamarin ya faru ne a garin Wenxing da ke yankin Sichuan.

'Yan sandan garin sun tabbatarwa BBC faruwar lamari, amma ba su yi wani karin bayani ba, suna mai cewa har yanzu ana kan binciken lamarin.

Wasu majiyoyin a garin sun ce yaron ya kashe mahaifiyarsa ne bayan da suka yi sa'insa a ranar Lahadi da daddare, a cewar kafar yada labarai ta Radio Free Asia.

Daga nan sai ya yanke mata kai ya sanya kan nata a cikin wani bokiti, kafin daga bisani ya jefa a cikin magudanar ruwa a waje, in ji Radio Free Asia.

Ta kuma ce ba a gano kisan gillar ba sai a ranar Laraba, lokacin da dan ajin su yaron ya nunawa iyayensa, wadanda ba su yi kasa a gwiwa ba wajen kai wa 'yan sanda rahoto.

An ce an kama yaron ne a makaranta.

Labarai masu alaka