Rikici ya barke a Birnin Kudus kan matakin Trump

man with arm in air as if he has just thrown a stone, with many other people behind him Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Palestinian protesters clashed with Israeli troops in Ramallah in the West Bank and further afield

Rikici tsakanin Yahudawa da Falasdinawa ya barke sakamakon matakin Donald Trump mai cike da ce-ce-ku-ce na mayar da Kudus babban birnin Isra'ila.

Rikici ya barke ne a Yammacin Kogin Jordan da Yahudawa suka mamaye da kuma Zirin Gasa, inda aka kashe wani Bafalasdine daya.

Majiyoyin yada labarai na Falasdinu sun ce mutum 200 ne suka ji rauni.

Tashin hankali na karuwa bayan wannan mataki na Shugaba Trump.

Isra'ila ce dai ta yabi wannan matakin nasa, amma kasashen Larabawa da na Musulmai sun yi Allah-wadai da shi.

Haka ma kawayen Amurka na kut-da-kut sun yi tur da matakin, wanda ya sauya matsayar Amurka a kan matsayin birnin Kudus.

Dama can Isra'ila na daukar Kudus a matsayin babban birninta, yayin da Falasdinawa suke daukar Gabashin Kudus a matsayin babban birninsu, wanda Isra'ila ta mamaye a yakin da aka yi a shekarar 1967 - a matsayin babban birnin Falasdinawa a nan gaba.

Amurka ce kasa ta farko da ta amince cewa Kudus ya zama babban birnin Isra'ila, tun bayan da aka kafa kasar a shekarar 1948.

A ina ake rikicin?

Dakarun Isra'ila sun yi arangama da Falasdinawa a biranen Bethlehem da Ramallah da Hebron da Nablus a Yammacin Kogin Jordan, da ma wasu kananan wuraren.

Hotunan talbijin daga Bethlehem sun nuna yadda ake amfani da motar ruwan zafi ana fesawa masu zanga-zangar da ke amfani da dutsuna wajen jifa.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Sharhi kan abun da Mr Trump ke nufi da ya ce zaman lafiya

Hayaki mai sa hawaye da bakin hayaki sakamakon kona taya ya cika sararin samaniya. Akwai kuma rahotannin da ke cewa dakarun na amfani da harsashin roba wajen harba wa mutane.

Irin hakan kuma na faruwa a wasu wuraren da ake samun fito-na-fito.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An kara yawan 'yan sanda a Gabashin birnin Kudus saboda zanga-zangar da ake tsammanin za a yi

Isra'ila ta girke karin bataliyar dakaru a Yammacin Kogin Jordan, sakamakon tsammanin cewa rikici zai balle bayan da shugabannin Falasdinawa suka yi kira da a yi zanga-zanga bayan sallar Juma'a.

A Gabashin Kudus kuwa ana wata hatsaniyar saboda daruruwan 'yan sanda da aka girke suna kokarin dakatar da masu zanga-zanga a wajen Tsohon Birni.

Zagayen tsohuwar katangar, wadda ke dauke da tsarkakakkun wurare dama sanannen waje ne na yawan yin arangama.

A kalla Falasdinwa 217 ne suka ji rauni a fito-na-fito din da aka yi a Yammacin Kogin Jordan da Gabashin Kudus, a cewar ma'aikatan lafiya na Falasdinu.

An kashe wani Bafalasdine dan shekara 30, yayin da wasu gomman Falasdinwan kuma suka ji rauni a Gaza, bayan da dakarun Isra'ila suka bude wa masu zanga-zangar da ke jifa da duwatsu wuta, a wata cibiyar sojoji da ke kan iyaka.

A wasu wuraren ma dai wannan mataki na Mista Trump ya jawo zanga-zanga sosai.

Dubban masu zanga-zanga da ke goyon bayan Falasdinu sun yi ta ihu a Jordan da Masar da Iraki da Turkiyya da kuma Iran.

Haka kuma masu zanga-zanga sun gudanar da ita a Malaysiya da Bangladesh da Pakistan da Afghanistan da yankin Kashmir na Indiya da kuma Indonesia, wadda ita ce kasar da ta fi yawan musulmai a duniya.

Ya ya duniya ta kalli matakin Trump?

An yi ta tur da Allah-wadai kan matakin Mr Trump musumman ma a kasashen musulmai.

Manyan kawayen Amurka na kut-da-kut kamar su Saudiyya da Masar da Jordan sun nuna kin amincewarsu, yayin da Masar da Bolivia da Faransa da Italiya da Senegal da Sweden da Birtaniya suka yi kira da a gudanar da taron gaggawa na Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya a ranar Juma'a, don tattauna mataki na gaba.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Shugabannin duniya sun yi wa Trump kashedi kan Kudus

Shugaban Falasdinu Mahmoud Abbas ya ce matakin Mista Trump abu ne da ba za a laminta ba, kuma wani babban jami'in Falasdinu ya ceba a maraba da mataimakin shugaban Amurka Mike Pence a Falasdinu, yayin wata ziyara da aka shirya da zai ziyarci yankin nan gaba cikin wannan watan.

Babbar makiyiyar Isra'ila wato Iran ta soki Donald Trump da son jawo yaki, yayin da kungiyar Hezbollah da Iran ke goyon baya a Lebanon ta yi kira ga Musulmai da kasashen Larabawa su goyi bayan sabuwar zanga-zangar Intifada.

Firayim ministan Isra'ila, Benyamin Natanyahu, ya ce Isra'ila ta matukar gode wa Mista Trump, wanda ya hada kansa har abadan ga tarihin babban birnin kasar, yayin da wasu Malaman Yahudawa na Isra'ila 250 suka sanya hannu a wata wasika ta nuna godiya ga Trump.

Me ya sa sanarwar ta ke da muhimmanci?

Birnin Kudus yana da muhimmanci ga 'yan Isra'ila da Falasdinawa. Birnin na kunshe da wurare masu tsarki na manyan addinai guda uku - Yahudanci da Islama da addinin Kirista.

Isra'ila ta mamaye bangaren Gabas - wadda a da ke karkashin mamayar Jordan a shekarar 1967, aka kuma kwace a 1980, amma duniya ta yarda da hakan.

Falasdinawa 330,000 ne suke zaune a Gabashin Kudus, tare da kusan Yahudawa 200,000 a gomman matsugunai a wajen.

Dokar kasa-da-kasa ba ta amince da matsugunan ba, duk da cewa isra'ila ba ta daukarsu a matsayin matsugunai na halal sai dai a matsayin unguwanni kawai.

An ruguza yarjejeniyar zaman lafiya ta Isra'ila da Falasdinu, za a cimma matsaya ta karshe ne kan batun Kudus nan gaba a wasu matakan tattaunawar zaman lafiya.

An ruguza zagaye na karshe na tattaunawa tsakanin Isra'ila da Falasdinu a shekarar 2014, kuma a yayin da Amurka take shirya sabbin kudurori, jami'an Falasdinu sun ce sanarwar Mista Trump ta sa ba za a iya sanya Amurkar cikin masu sasantawa ba nan gaba.

Image caption Manyan wuraren ibada a tsohon birnin Kudus

Labarai masu alaka