Abin da ya faru a Afirka makon jiya

Zababbun hotunan abubuwan da suka faru a Afirka makon jiya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A ranar Talata ne wata mata ta dauki hoton kanta lokacin da mata suka yi zanga-zanga kan bukatar a karfafa musu gwiwa ta hanyar sana'o'i a birnin Abuja da ke Najeriya
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A ranar Laraba ne Fifi Loukoula na Congo-Brazzaville ya samu kai wa zagaye na gaba a gasar daga karfe ta duniya da ake yi a Mexico
Hakkin mallakar hoto Empics
Image caption A ranar Talata ne 'yar kwallon hannu ta Kamaru Vanessa Djiepmou ta yi nasara a Leipzig da ke kasar Jamus
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A ranar Alhamis ne wata 'yar Senegal take rawa lokacin bikin bude sabon filin jirgin sama a babban birnin kasar Dakar
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A ranar Laraba ne aka daukin hoton mawaki dan kasar Saliyo Janka Nabay a dakin wake-wake na Le Libert a birnin Rennes da ke Faransa
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A ranar Alhamis ne mutane suka leko kallon shugaban Faransa Emmanuel Macron
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Emmanuel Macron ya kai ziyara karon farko yankin da suke neman 'yancin kai daga Faransa
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A ranar Alhamis ne wadansu masu zanga-zanga suka kona tutar Amurka a Tunisiya
Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption A ranar Asabar ne 'yan ci rani suka yi zanga-zanga a kan rahoton da aka samu na sayar da su a matsatin bayi a kasar Libya
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A ranar Talata ne aka dauki hoton wata 'yar Najeriya bayan an dawo da ita gida a kokari da take na tsallakawa kasar Turai ta tsallakawa ta Libya
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A ranar Talata ne wadansu yara suke zana hoton Shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir a babban birnin kasar Juba
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A ranar Litinin ne aka saka hoton Emmerson Mnangagwa a gidan gwamnatin Zimbabwe, bayan kwana 10 da rantsar da shi a matsayin shugaban kasa
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A ranar Lahadi ne wani yaro yake kewayawa a cikin babban dakin fadar Mobutu Sese Seko tsohon Shugaban Zaire., inda yanzu ake kira Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo
Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption A ranar Lahadi ne farin wata ya haskaka wani tsauni a Afirka ta Kudu
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A ranar Asabar ne wata take duba wayarta a makon tallan kayan kawa na Swahili da aka yi a Dar es Salaam babban birnin Tanzaniya
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A ranar Asabar ne aka yi makon tallan kayan kawa na shekara-shekara da ake yi Dar es Salaam, babban birnin Tanzaniya
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu maza masu tallan kayan kawa lokacin a lokacin makon kayan ado na Swahili a birnin Dar es Salaam
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sabon Jakadan Najeriya a kasar Birtaniya, George Adesola Oguntade, yayin da ya gabatar da takardar kama aiki ga Sarauniyar Ingila Elizabeth II a fadarta ranar Laraba

Labarai masu alaka