Adikon Zamani: 'Dole ne mace ta yi wa mijinta girki?'
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Adikon Zamani: 'Dole ne mace ta yi wa mijinta girki?'

Ku latsa alamar lasifikar da ke sama don jin muhawarar da aka tafka kan wannan batu, da ma matsayar malaman addini a kanta.

Adikon Zamani tare da Fatima Zahra Umar

Shin dole ne sai mace ta yi wa mijinta girki?

Wannan wata muhawara ce da ba za ata taba karewa tsakanin mata da maza ba, kan ko aikin waye a aure ya dafa abinci, wanda shirin Adikon Zamani na wannan mako ya mayar da hankali a kai.

A wannan mako mun ji ra'ayoyin mata kan ko mene ne tunaninsu a kan wannan batu.

Shin yi wa miji girki dole ne ko kyautatawa ce?

Akwai wadanda suka yarda cewa yin girkin mace kyautatawa ce da take yi tsakani da Allah amma ba wai dole ba.

Ga wadanda suka yarda da wannan batun, dole ne namiji a matsayinsa na wanda ke da hakkin wadata iyalinsa da abinci to ya wadata su da komai da ake bukata don yin girki.

Wasu kuwa a ganinsu, girki wani aiki ne da mata suke yi ba tare da ana gode wa kokarinsu ba, duk da cewa suna daukar lokacinsu ne da ya kamata su yi wasu abubuwan daban.

Wadannan mutanen sun yi amannar cewa ana amfani da irin wadannan abubuwa ne wajen rage kimar mata da cewa aikin abinci ne aikinsu.

Suna ganin cewa girki wata baiwa ce da ya kamata a ce ko wanne dan adam ya iya, ba wai a dinga danganta shi da mata ba kawai.

Akwai kuma wadanda suka yi amanna cewa hanya mafi kyau ta kula da miji ita ce ta yi masa girki.

Masu wannan ra'ayin sun yi amannar cewa girki abun alfaharin mace ne, kuma bai kamata mace ta yi wasa da dafawa mijinta abinci ba, har sai ranar da mutuwa ta raba su.

Irin wadannan mutanen sun yi amannar cewa duk macen da ba ta yi wa mijinta girki to ta yi asara kuma ta zama abun kunya ga mata.

Sannan kuma akwai wasu matan da suka yi amanna cewa ba lallai ne a mayar da girki tilas a kan mace ba.

Suna so mace ta samu damar zabin yi wa mijinta girki ko kuma ka da ta yi. Sun rage nauyin da al'umma ta dorawa mata na cewa tilas ne su yi girki.

Abun da suke gani shi ne bai zama lalle a tilastawa mace yi wa mijinta girki ba idan har ranta ba ya so.

Za ku yi tunanin cewa wannan muhawarar ba ta da wani amfani. Aure da yawa sun mutu saboda mace ta gazawa yi wa mijinta girki mai dadi.

Aure da yawa sun mutu saboda mace ta ki yi wa mijinta girki. Na taba jin labarin wani mutum da ya yi wa matarsa saki uku saboda ta sa mai aikinta ta dafa masa abincin dare.

Kwarai wasu mutane na daukar irin hakan da zafi.

Wannan ya fi gaban fada tsakanin mata da maza; batu ne na ainihin abun da ke faruwa a rayuwa.

To ku a wanne bangare ku ke? Dole ne mace ta yi wa mijinta girki?

Ku aiko mana da tsokacinku!