Kun san birnin da mazaunansa ba sa fushi?

Daga Megan Frye

Zai yi wuya ka ga dan Mexico City ya bata rai a bainar jama'a Hakkin mallakar hoto John Mitchell/Alamy)
Image caption Zai yi wuya ka ga mazaunin birnin Mexico City ya bata rai a bainar jama'a

Na zauna a birnin Mexico City har kimanin wata shida kafin na ga wanda ya yi fushi a bainar jama'a.

Kuma mutumin ba dan kasar Mexico ba ne.

Lamarin ya faru ne bayan an kammala aikin ranar, kuma kantin shan shayi mai cike da mutane da nake ciki a wancan lokacin jerin mutane ya mamaye teburinsa.

Nan da nan sai wani mutum ya fara daga muryarsa ga mai karbar kudi: "kana son ka yi mini fashi!" ya yi ihu cikin harshen Spaniyanci, mara karin harshen Mexico.

Ya kalli kantin shan shayin, sannan ya yi shelar cewa ya bai wa mai karbar kudin kudin Peso 500, amman canjin Peso 200 kawai ya karba.

Da alama hankalin matashi mai karbar kudin ya tashi, kuma mutanen da ke layi sun mayar da hankalinsu kan kafafunsu ko kuma akwatin nuna kayan mako-lashe dangin fulawa da ke gabansu.

"Wannan abin mamaki ne!" mutumin ya ci gaba da ihu, yana mai juya akalar fushi da takaicinsa ga dukkan mutanen da ke cikin kantin shan shayin. "wannan laifi ne."

Babu wanda ya kawo masa dauki. Kowa dai ya yi matukar mamakin cewa zai iya daga muryarsa da karfi haka.

Daga karshe, mai karbar kudin ya juya kuma ya shiga dakin baya. Mutmin ya yi huci na wani minti kafin ya bar gidan shan shayin cikin fushi.

Hakkin mallakar hoto Lucas Vallecillos/Getty Images
Image caption Ana yi wa Mexico City kallon daya daga cikin biranen kasashen Latin da suka fi kasancewa na zamani da masu yawan mutane daban-daban

Da zaran ya fice, mai karbar kudin ya dawo ya yi murmushi ga abokin hulda na gaba kuma ya ci gaba da sayar wa mutane abubuwa kamar yadda ya saba.

Ban san daga ina wannan mutumin ya fito ba, amman a karara take cewa ba daga Mexico yake ba, ko kuma wani wuri da ke kusa da Mexico.

Zai yi wuya ka ga dan Mexico ya fice daga hayyacinsa ta hanyar fushi sai dai in ya sha barasar mai yawa.

Wannan ya kasance ne saboda abu biyu ne ba in da za su kai ka a Mexico: nuna fushi a bainar jama'a da kuma fito-na-fito.

Tun suna yara, ake koyawa 'yan Mexico kada su rinka nuna fushi.

Wata karin maganar Mexico na cewa 'El que se enoja pierde' ma;ana' tana nufin: 'wanda ya ba ta rai, zai yi asara.'

Hakkin mallakar hoto Tony Anderson/Getty Images
Image caption Wata karin maganar Mexico na cewa 'El que se enoja pierde' ma;ana tana nufin 'wanda ya bata rai, zai yi asara.'

"An koya mana cewa muna bukatar kasancewa cikin nitsuwa a ko wane hali," in ji Eleazar Silvestre.

Kuma an fi daukar wannan shawarar da muhimmanci a tsakiyar kasar ciki har da Mexico City wadda ake yi wa kallon daya daga cikin biranen kasashen Latin da ya fi kasancewa na zamani da kuma hada mutane daga wurare daban-daban.

Al'adar mutane a birnin Mexico City na kunshe da girmamawa a bainar jama'a wanda ban taba ganin irinta ba a sauran biranen da suka kai shi.

Tabbas, ya kamata tashin hankali ya yi yawa duba yadda kimanin mutum miliyan 25 ke yawo a birnin a ko wace ranar.

Amman a nan wani irin hatsaniya mai tsari da ya dogara ga gaisuwa da kuma tsabar hakuri.

Labarai masu alaka