Zargin fyade: Shugaban kasa zai aika - Mataimakinsa

Zuma Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Jacob Zuma ya zama shugaban Afirka ta Kudu shekara uku bayan an wanke shi daga zargin aikata fyade

Wani babban dan takara da ke yunkurin maye gurbin Shugaba Jacob Zuma a matsayin jagoran jam'iyyar ANC mai mulkin Afirka ta Kudu ya ce ya yarda da matar da ke zargin Mista Zuma cewa ya yi mata fyade sama da shekara goma da ta wuce gaskiya ta fada.

Mataimakin Mista Zuma, Cyril Ramaphosa, ya fada wa wani gidan rediyon kasar: "Eh, Zan yarda da ita."

A shekara ta 2006 ne aka gaza samun Mista Zuma da laifin yin fyade ga Fezekile Kuzwayo - 'yar wani tsohon abokinsa.

Ya ce da yardarta ya kwanta da ita.

Mista Ramaphosa na takara ne da tsohuwar mata Zuma, wato Nkosazana Dlamini-Zuma, don zama jagorar ANC a wata fafatawa da za a fara ranar Asabar mai zuwa.

Dan takarar da ya yi nasarar zama shugaban jam'iyyar zai samu kyakkyawar dama kasancewa sabon shugaban Afirka ta Kudu a 2019.

Sharhi - Lebo Diseko, Johannesburg

Akwai dai mabambantan ra'ayoyi game da kalaman Mista Ramaphosa a kan zarge-zargen yin fyade ga Misis Kuzwayo.

Wasu sun yaba masa a kan fitowa baro-baro a martaninsa ba tare da inda-inda ba, idan an kwatanta da abokiyar takararsa da ke neman shugabancin ANC Lindiwe Sisulu.

Da aka yi mata wannan tambaya, sai ta ce: "Na amince idan ta yarda an yi mata fyade".

Sai dai mutane da dama a shafukan sada zumunta sun tambaya me ya sa Mista Ramaphosa bai fito bainar jama'a ya goyi bayan Misis Kuzwayo lokacin da take da rai ba.

Mutane dai na sake nuna sha'awarsu ga wannan shari'ah ta fyade, bayan fito da wani littafi da ke bayani dalla-dalla kan al'amuran rayuwar Misis Kuzwayo.

Musammam jama'a sun fusata kan zargin muzantawar da jami'an jam'iyyar ANC mai mulki suka yi mata a lokacin.

Yayin wata zantawa a rediyo, Mista Ramaphosa ya yaba wa karfin halin Misis Kuzwayo na kai kara gaban kotu, ya ce:

"Na san irin wahala da ciwon da ke akwai, ga mace ta yi karfin hali ta budi baki ta ce: 'Eh an yi min fyade'. Jazaman hakan na daya daga cikin shawarwari mafi wahala da ta yi a rayuwarta."

Misis Kuzwayo, wadda Mista Zuma ya ba wa fikon shekara 32, ta tsere zuwa ketare kuma daga bisani ta mutu bayan ta yi fama da doguwar jinya, amma wakilin BBC a Johannesburg Andrew Harding ya ce takaddama a kan shari'ar har yanzu ba ta kau ba.

Misis Kuzwayo ta kamu da kwayar cuta mai karya garkuwar jiki kuma bahasin Mista Zuma lokacin wannan shari'ah, na cewa sai da ya yi wanka bayan jima'in da ya yi matar ba tare da kwaroron roba ba saboda gudun kamuwa da cuta, ya sanya mutane dariya.

Da yake wanke Zuma daga laifi, alkalin ya karkare da cewa: "Mai karar ta cika son zargin maza da yi mata fyade ko kuma yunkurin yi mata fyade."

Labarai masu alaka